Jam’iya mai mulki a Nijeriya ta sanya ranar Litinin 13 ga watan Afirilu na shekarar 2026 domin soma zaben mazabu a jihohin Adamawa da Zamfara da kuma Abuja.
Sai kuma 16 ga wata za a yi zaben kananan hukumomi, bayan kammalawa, 18 ga wata a yi zaben shugabanni a matakin jiha.
Bayan jam’iyar ta kammala zabe a jihohi 32 na Nijeriya a yanzu ta sanya lokacin gudanar zaben wadannan da ta dakata zabensu saboda shigowar gwamnonin jihohin guda biyu.
Sanya zaben ba tare da jihar Rivers ba hakan ke nuna har yanzu ba a kammala rikicin shugabanci a can ba, hakan na kara nuna akwai kalubale a jam’iyar APC.




