Home Rahoto ‘Yan sanda sun kashe Lakurawa, sun ƙwato shanu 33 a Kebbi

‘Yan sanda sun kashe Lakurawa, sun ƙwato shanu 33 a Kebbi

2
0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, sun kashe ‘yan ta’addan Lakurawa da suka kai hari Ƙaramar Hukumar Dandi.

‘Yan ta’addan sun farmaki wani gidan gona ne, inda suka kora dabbobi ciki har da shanu 33, sai dai rundunar tsaron haɗin guiwa sun daƙile harin.

‘Yan sandan jihar Kebbi sun yi nasara hana ‘yan bindiga tafiya da shanu 33 da suka sata kan hanyar Kamba zuwa Kangiwa a karamar hukumar Dandi.Harin da ya faru a ranar Jumu’a in da ‘yan bindigar da ake tsammanin Lakurawa ne suka saci dabbobin suka gudu da su.

‘Yan sandan garin Kamba a cikin hanzari suka fuskanci batagarin hakan ya cilasta suka barin dabbobin ba wani jam’iin dan san sanda da ya samu rauni.

A farmakin an samu nasarar jikkata dan bindiga guda, dayan ya tafi da rauni a jikinsa, an yi nasarar kwato dabbobi 33, za a cigaba kokarin kamo wadanda suka tsere.

Kwamishinan ‘yan sanda Umar M. Hadeja ya yabawa jami’an kan kokarin da hadin kansu.

A bayanin da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Bashir Usman ya fitar ya ce hukumar za ta cigaba da goyon bayan jami’anta masu kwazo ta yi kira ga jama’a su rika ba da bayani sahihi a kan lokaci domin ganin an yi nasarar kawar da batagari.

Abbakar Aleeyu Anache

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here