Jam’iyyar ADC ta ce ba ta amince da yadda Hukumar Zabe ta Nijeriya (INEC) ta fassara hukuncin Kotun Daukaka Kara ba, tana zargin cewa an matsa wa hukumar lamba daga gwamnati.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na kasa na jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce matakin na INEC ya saba da gaskiya.
ADC ta zargi INEC da nuna bangaranci, tana mai cewa hukumar ta karkata zuwa bangaren gwamnati a maimakon tsaya wa gaskiya da ‘yan kasa.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa tana duba matakan da za ta dauka nan gaba, tare da kira ga mambobinta da sauran ‘yan Nijeriya da su ci gaba da kasancewa cikin shiri yayin da ake jiran mataki na gaba.




