Home Siyasa ADC na ƙoƙarin cimma matsaya guda kan ɗan takarar shugaban ƙasa na...

ADC na ƙoƙarin cimma matsaya guda kan ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027 — Bolaji Abdullahi

11
0

Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa tana kokarin daukar hanyar cimma matsaya guda wajen zaben dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027.

Sakataren yaɗa labarai na kasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin wata hira a shirin “One-on-One” na gidan talabijin na Arise a ranar Asabar.

Abdullahi ya ce jam’iyyar na da zabin gudanar da zaben fidda gwani kai tsaye ko kuma cimma matsaya guda, yana mai cewa an cire zaben wakilai (indirect primaries) daga cikin zabin da ake da shi bisa dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.

Ya kara da cewa hanya mafi dacewa ga jam’iyyar ita ce cimma matsaya guda saboda rage kashe kudi.

A cewarsa, “Muna kokarin yadda za mu iya cimma matsaya guda domin ita ce mafi saukin kudi a gare mu, kuma shi ne mafi alheri a halin yanzu.”

Sai dai Abdullahi ya soki jam’iyyar APC mai mulki, inda ya ce karfinta yana da alaka da shugabancinta na yanzu.

Ya ce idan aka cire iko daga APC, jam’iyyar za ta ruguje cikin sauri, yana mai cewa Bola Ahmed Tinubu ne ginshikin da ke rike jam’iyyar.

Ya kuma bayyana APC a matsayin wata jam’iyya da aka kirkira ne domin cimma wasu manufofi na musamman, musamman tabbatar da mulkin Muhammadu Buhari da kuma Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here