Mataimakin Kodineta na Atiku da Dauda a zaɓen 2023 da ya gabata Honarabul Yusuf Abdullahi Bakura da aka fi sani da MD ya soki komawar Gwamnan Zamfara a jam’iyyar APC in da yake ganin hakan ba da yawun mutanen Zamfara aka yi ba domin jama’ar jihar basa goyon bayan gwamnatin APC a matkin ƙasa.
Homabul Yusuf MD a hirarsa da waƙilinmu a satin nan ya ce “Gwamna Dauda bai koma APC don cigaban mutanen Zamfara ba, ya yi haka ne don ya tsira da laifukansa na mulki, ba mu yi mamakin komawarsa ba saboda tsintattar mage ba ta mage gidansu ne ya koma, an zaci adali ne aka dauko shi da taimakon Allah ya yi nasara sai ya riƙa zalunci.
“Tsohon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya ce Dauda ya karɓi kuɗi kusan Tiriliyan ɗaya amma ba abin a zo a gani don haka sai Gwamnan ya yi bayani kansu, tun sannan ya razana ya ga bari ya koma cikinsu don ya ci bilis, yanzu ya koma cikin azaluman da yake zagi komai ya faɗa kansu, ya ce wai yayi haka ne don tsaro ba gaskiya ba ne domin Katsina da Sakkwato da Neja da Borno da Kebbi da Kaduna duk APC ke mulki a wuraren mi ya canja da har Zamfara za ta so ta koma APC don a samu a harkar tsaro. Da man mutane sun zaɓe shi ne don ya nuna zai iya magance matsalar tsaro ashe ba haka ba ne ya fi na baya zalunci.
“Mu ya zalunce mu duk wani dan PDP a Zamfara bai kyauta masa ba haƙƙinmu na kansa kuma sai Allah ya ƙwatar mana abinmu ya wahalar da mu, duk wanda ya yi PDP a Zamfara bai taimake shi ba don yana da wannan ƙudirin, APC yake yi wa aiki tun farko mun sani don da mu ake siyasar.
“Ba don PDP na da matsala ne ya barta ba don su ne suka haifar da matsar tun farko, shi dai ya tafi ya karɓi nasa kaso da ake baiwa gwamna da ya yi wanka ya kuma samu mafaka,” a cewarsa.
Kan maganar samar da filin jirgin sama a Gusau ya ce “filin jirgi ne matsalar Zamfara a lokacin da muke yaƙin neman zaɓe abin da muka nemi mutane su zaɓe mu kan shi matsalar tsaro ne ya ce ya san hanyar da za a bi a magance matsalar tsaro kan haka talakan Zamfara ya zaɓe shi a yanzu matsalar ta fi yanda ya gade ta, akwai abubuwa da yawa da suke addabar Zamfara ba filin jirgi ba, kamar matsalar tattalin arziki da rashin aikin yi, ba a riƙa yin kwamitocin da ba a saurare ba, ko ba da kwangila da mutanen jiha ba su amfana, mafiyawan waɗanda suka goya bayansa sun bar gari don talauci.
“Tarihi zai maimaita kansa da ikon Allah sai an kayar da Dauda a zaɓe mai zuwa tun da yafi waɗanda ya gada zalunci, abin da Matawalle ya samu a shekara huɗu ya same shi a wata uku, ya tafi APC amma ba tare da mu ba za mu tafi jam’iyyar da ta dace da mu da al’umma suke so kuma za mu yi nasara da yardar Allah domin Gwamnatin Dauda ta zalunci al’umma ba a magance matsalar tsaro da tattalin arziki da rashin aikin yi ko ɗaya bai yi ba,” kalamansa.




