Zainab Kassim, tsohuwar mataimakiya ta musamman ga uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari, ta garzaya kotu bisa zargin yin garkuwa da ita da kuma cin zarafinta a fadar shugaban kasa.
Misis Kassim ta yi hidima ga uwargidan shugaban kasa na tsawon shekaru hudu daga watan Yuni 2015 zuwa Satumba 2019.
Daga bisani an naɗa ta a matsayin mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa a ofishin uwargidan shugaban kasa daga Satumba 2019 zuwa Fabrairu 2022, lokacin da aka sallame ta.
A wata sanarwa da lauyanta, ‘Deji Ajare, ya sanyawa hannu, Misis Kassim ta ce jami’an tsaro na farin kaya, SSS ne su ka yi awon-gaba da ita zuwa fadar shugaban kasa, inda uwargidan shugaban kasar ta lakaɗa mata duka.
Ta bukaci a biya ta diyyar Naira miliyan 100 da kuma dawo mata da wayarta ƙirar 20 Ultra da aka kwace mata.




