Daga Mohammed Awwal Umar
Babbar jam’iyyar adawa ta ADC ta bayyana kudurinta na fara rajistan yayan jam’iyya a jihar Neja. Shugaban jam’iyyar a Alhaji Musa Hassan ne ya bayyana hakan lokacin da ayarin manema labarai suka tuntube kan maganar rajistan yayan jam’iyya duba da lokuttan da hukumar zabe wasu rahotanni na bayyanawa cewar ta tsayar da ranar zaben fidda gwani na jam’iyyu.
Alhaji Musa Hassan, yace mu a jam’iyyance maganar rajistan yayan jam’iyya muke, duba da cewar wasu jahohin sun dade da farawa, amma mu a jihar Neja yanzu muke son farawa mu kammala cikin sati uku.
Uwar jam’iyya ta kasa ta kafa kwamitin da zai kula da wannan aikin, karkashin shugabancin tsohon dan majalisar dokokin tarayya, Hon. Baba Shehu Agaie, bayan nan kowani shiyya na shiyyoyi uku na jihar nan an bada Shugaba musamman sune zasu sanya idanu na ganin yadda aikin rajistan zai kasance.
Injiniya Mukhtar Suleja tsohon dan majalisar dokokin tarayya shi, zai jagoranci yankin Neja ta tsakiya, saboda rahoton da ke yawo cewar akwai wani bangare da ke Kodinetin wannan rajistan yayan jam’iyya, to ba masu gaskiya ba ne yan kutse ne.
Alhaji Musa Hassan, saboda karbuwar jam’iyyar nan a gurin al’ummar Neja, lokacin hadaka wadanda suka shigo hadaka da jam’iyyar ADC suka kama wannan sabon sakatariyar da muke tattaunawa da ku yau.
Yanzu jam’iyyar ADC ta baro tsohon sakatariyar ta na Three Arm Zone zuwa wannan sabon guri, Eastern Bye Pass daura da rukunin gidajen M.I. Wushishi, wanda duk wani da ya kamata jam’iyya tayi hukumance kafin mu dawo nan mun kammala shi.
A matsayina na shugaban jam’iyyar nan ta ADC a jihar Neja, ba wani abu da zan aiwatar a jam’iyyance dole sai abinda NEC ta amince da shi. Rt. Hon. Baba Shehu Agaie shi na sani shugaban kwamitin kula da wannan rajistan a jihar Neja, kuma Injiniya Mukhtar Suleja shi ne shugaban kwamitin a yankin Neja ta tsakiya, kuma kamar yadda na fada a baya wannan aikin zai dauki adadin sati uku ne za a kammala shi.
Dangane da zaben shugabannin jam’iyya kuwa, duk wata sanarwa da ka gani bugi ce, domin a hukumance hukumar zabe ba ta sanar da mu yayan jam’iyyun siyasa ba. Saboda abinda ke da muhimmanci kawai mallakar katin zama dan jam’iyya ta hanyar yin rajista da jam’iyyar ADC, Amma a yau da za ka rubuta takardar barin jam’iyyar da ka ke yi zuwa ADC ka samu rajista a yanzu daidai ka ke da wanda aka faro tafiyar jam’iyyar nan da shi.
Yanzu ba maganar Coalition, maganar jam’iyya ce kawai. Saboda haka mu jam’iyyar ADC a jihar Neja a dunkele muke babban aikin da muka sanya gaba shi ne kawo cigaban tsarin dimukuradiyya a jihar nan. Jam’iyyar dai ta shelanta ranar 24 ga watan nan a matsayin ranar da ta ware dan rantsar ADC Coucos na jihar Neja wanda ya shafi wakilcin dukkanin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar Neja.






