Home Siyasa Tambuwal ya fice daga jam’iyar PDP

Tambuwal ya fice daga jam’iyar PDP

4
0

Tsohon gwamnan Sakkkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya fice daga jam’iyar PDP.

A wata takarda da Sanata Tambuwal ya sanyawa hannu da Kansa a ranar Laraba da ya aikewa shugaban  jam’iyar PDP a mazabarsa ta Shimfiri a karamar hukaumar Tambuwal ya ce ya  fice daga PDP domin matsalolin da take fama da su na rayuwar Kai da sauran rikicin cikin gida.

Tambuwal bai sanar da jam’iyar da Zai shiga ba amma alamu ya nuna Zai shiga ADC ne ganin yadda hulda mai kyau ke tsakaninsa da jagororin tafiyar.

Tambuwal ya halarci tarukkan ADC da dama a Abuja da wasu jihohi abin da ke nuna in da lamarin siyasarsa zai karkata.

Sanata Tambuwal shi ne jagoran adawa a jihar Sakkkwato da zai kalubalanci gwamnati mai ci ta APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here