Home Siyasa DALILIN DA YA SA NA KOMA JAM’IYYAR APC – GWAMNA DAUDA LAWAL

DALILIN DA YA SA NA KOMA JAM’IYYAR APC – GWAMNA DAUDA LAWAL

2
0

DALILIN DA YA SA NA KOMA JAM’IYYAR APC – GWAMNA DAUDA LAWAL

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa rikicin cikin gida da kuma taƙaddamar shari’a da ke addabar jam’iyyar PDP ne babban dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar.

Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Mallam Mani Mummuni, ne ya sanar da ficewar a hukumance a ranar Litinin bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Gusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa sauya sheƙa daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC wani mataki ne da ya zama dole domin alheri da cigaban al’umma.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa shiga Jam’iyyar APC shawara ce da masu ruwa da tsaki a Jihar Zamfara suka yanke sakamakon matsalolin shari’a da Jam’iyyar PDP ke fuskanta.

Sanarwar ta ce a wani ɓangare:

“Jiya, Gwamna Dauda Lawal ya sanar a hukumance cewa ya sauya sheƙa daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC, bayan yanke wannan shawara tare da amincewar dukkan masu ruwa da tsaki a Jihar Zamfara.

“Gwamna Dauda Lawal ya nuna cikakken biyayya da jajircewa ga jam’iyyar PDP. Ya yi ƙoƙari sosai wajen sasanta ɓangarorin jam’iyyar domin a samu haɗin kai tare da tabbatar da cewa jam’iyyar ta tsaya tsayin daka wajen tsayar da ‘yan takara a zaɓuka masu zuwa.

“Duk da haka, ƙoƙarin samar da zaman lafiya, sulhu, da warware matsalolin ba tare da zuwa kotu ba ya gamu da cikas, lamarin da ya jawo jerin shari’o’i da ka iya haifar da matsaloli nan gaba, musamman ga shugabannin da za su tsaya takara a zaɓukan shekarar 2027.

“Gwamna Dauda Lawal shi ne mutum na ƙarshe da ya tsaya daram a cikin Kam’iyyar PDP har zuwa ƙarshe, wanda hakan ya kai ga hukuncin da Kotun Ɗaukaka Kara ta yanke jiya.

“Shi ne gwamna ɗaya tilo da ke neman wa’adi na biyu da ya zaɓi ci gaba da zama a jam’iyyar, yana fatan shugabannin jam’iyyar za su nuna nagarta tare da ɗaukar matakan da suka dace.

“A cikin wasu jerin tarurruka da suka ɗauki makonni ana yi, Gwamna Dauda Lawal ya sanar da masu ruwa da tsaki cewa ya amince da buƙatarsu ta komawa jam’iyyar APC, amma zai yanke hukunci ne bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Kara.

“Kotun Ɗaukaka Kara da ke Abuja a ranar Litinin ta yi watsi da karar da PDP ta shigar kan hukuncin da Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke a ranar 31 ga Oktoba, wanda ya hana Hukumar Zaɓe mai zaman kanta (INEC) amincewa da sakamakon babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba.

“Hukuncin Kotun Daukaka Kara ya kawo karshen zaman Gwamna Dauda Lawal a jam’iyyar PDP, inda ya fifita muradun Jihar Zamfara. Ya shiga jam’iyyar APC domin ci gaba da aiwatar da kudurin Ceto da Sake Gina Zamfara.”

SULAIMAN BALA IDRIS
Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara
10 ga watan Maris, 2026.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here