Home Uncategorized Matukar Gwamna Ya Dauki Gyaran Matsalar Tsaro Ba Tashi Ba Ce Harkar...

Matukar Gwamna Ya Dauki Gyaran Matsalar Tsaro Ba Tashi Ba Ce Harkar Ba Za Ta Gyaru Ba—–Ibrahim Liman

6
0
 
Dan takarar Gwamna a jam’iyar ADP a Sakkwato Ibrahim Muhammad Liman Sifawa ya fadi yanda za a magance matsalar tsaro a jihohin Nijeriya in dai har da gaske ake yi kan matsalar dole ne gwamna ya dauki harkar tsaro tasa ce ba gwamnatin tarayya ba.
Ibrahim Liman a muhawarar ‘yan takarar gwamnan Sakkwato da gidan Rediyon VOA ya shirya aka gudanar a cikin jami’ar Usman Danfodiyo dake Sakkwato ya ce wai sai ka ji gwamna ya fadi harkar tsaro ba ta sa ba ce bayan kuma shi ne shugaban tsaro a jiha.
Ya ce harkar tsaro bayan gwamna ya aminta aikinsa ne ya samar da tsaro aka ji tsoron Allah ya rike amana kan gudanar mulki hakan zai sa a magance matsalar tsaro in da ake fama da su.
Liman in ya samu dama ya ce zai yi aiki da dubaru na kwarewa domin magance matsalar tsaro a jihar Sakkwato. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here