Home Rahoto Gwamnatin Tinubu Ta Gano Talakawan da Suka Fi Bukatar Taimako a Najeriya

Gwamnatin Tinubu Ta Gano Talakawan da Suka Fi Bukatar Taimako a Najeriya

2
0


Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ci gaba xa kokarin yakar talauci a Najeriya. Gwamnatin ta yi ikirarin cewa zuwa yanzu, ta kammala gano mutanen da suka fi ko wadanne fama da talauci da kuncin rayuwa. 
Ministan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Dr. Bernard Doro, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a cikin shirin ‘The Morning Show’ na tashar Arise TV a ranar Juma’a, 13 ga watan Fabrairu, 2026. 
Dr. Doro ya bayyana cewa gwamnatin Tarayya ta yi nasarar gano gidaje mafi talauci a Najeriya ta hanyar rijistar jin-ƙai ta ma’aikatarsa. Ministan ya ce tsarin tantancewar da aka yi amfani da shi a aikin hada rijistar, ya dogara sosai da bayanan al’umma wajen gano waɗanda suka fi buƙatar taimako a fadin kasar nan. 

A cewarsa, rijistar jin-ƙai a halin yanzu ta ƙunshi bayanan gidaje marasa galihu miliyan 17.9, wanda ke wakiltar kimanin ’yan Najeriya miliyan 70. “An hada rijistar ne tare da haɗin gwiwar al’umma. Galibi mun fi dogaro da bayanan da muka samu daga al’umma, ta hanyar amfani da ka’idojin tattalin arziki da zamantakewa. “Ta haka muke..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here