Home Rahoto Malami ya yi wa kotu bayanin yadda ya samu kuɗinsa

Malami ya yi wa kotu bayanin yadda ya samu kuɗinsa

4
0

Tsohon Babban Lauyan Ƙasa (Attorney-General of the Federation and minister of justice),

Abubakar Malami SAN, ya shaida wa kotu cewa ya samu ₦374m daga albashi da alawus-alawus, ₦10.17bn daga harkokin kasuwanci masu zaman kansu, da kuma ₦958m a matsayin kyaututtuka daga abokan sa na ƙashin kai. Ya bayyana hakan ne yayin da yake neman kotu ta soke umarnin wucin-gadi da ya bayar na ƙwace kadarori 57 da ake danganta masa.

Malami ya bayyana wannan ta bakin lauyansa, Joseph Daudu, wanda ya gabatar da bukatar (motion on notice) a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ake roƙon kotu ta soke umarnin wucin-gadi da aka bayar kan kadarori uku daga cikin kadarori 57 da EFCC ta ƙwace domin a mallaka su ga Gwamnatin Tarayya.

Lauyan ya sanar da kotu cewa Malami ya bayyana dalla-dalla hanyoyin samun kuɗinsa a takardar bayyana kadarori da ya miƙa wa CCB, inda ya haɗa da abubuwa masu zuwa:

₦374,630,900 daga albashi, estacodes, alawus ɗin rabuwa da aiki (severance allowance), da sauransu.

₦574,073,000 a matsayin kuɗin da aka samu daga sayar da kadarori.

₦10,017,382,684 a matsayin juyin kuɗin kasuwanci (turnover) daga harkokin kasuwanci.

₦2,522,000,000 a matsayin rance (loans) da aka ba kasuwanni.
₦958,000,000 a matsayin kyaututtukan gargajiya daga abokan sa na ƙashin kai.

₦509,880,000 a matsayin kuɗin shiga da aka samu daga ƙaddamarwa da gabatar da littafinsa mai taken:

“Contemporary Issues on Nigerian Law and Practice, Thorny Terrains in Traversing the Nigerian Justice Sector: My Travails and Triumphs.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here