Home Siyasa Shattima na zawarcin Gwamnan Bauchi da Adamawa su shiga APC

Shattima na zawarcin Gwamnan Bauchi da Adamawa su shiga APC

7
0

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana jin dadinsa game da sauya sheƙar Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas. 

Shettima ya ce sauya shekar Kefas zuwa jam’iyyar APC a matsayin abin alfahari da ya taba zuciyarsa ƙwarai.

Shettima ya yi wannan jawabi ne a Jalingo, babban birnin Taraba, yayin bikin tarba na musamman da aka shirya domin maraba da gwamnan cikin jam’iyya mai mulki, cewar Vanguard. 

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya nuna fata cewa gwamnoni a jihohin Adamawa da Bauchi za su sake duba matsayinsu su mara wa APC baya. 

A wajen taron, Shettima ya ayyana Gwamna Kefas a matsayin jagoran APC a Taraba, tare da kiran mambobin jam’iyyar su mara masa baya. 

Ya ce goyon bayan jam’iyya zai ƙarfafa gwamnan wajen haɗa kan al’ummar jihar da kuma samar da ribar dimokuraɗiyya ga jama’a. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here