Home Siyasa Sokoto: Sanata Lamiɗo ya bayyana ƙudirinsa na takarar Gwamna a 2027

Sokoto: Sanata Lamiɗo ya bayyana ƙudirinsa na takarar Gwamna a 2027

2
0

Sanata Ibrahim Lamiɗo ɗan majalisar dattijai dake waƙiltar yankin Sokoto ta gabas a zauren Majalisa ya bayyana ƙudirinsa na neman kujera Gwamnan Sokoto a kakar zaɓe mai zuwa ta shekarar 2027.

Sanata Lamiɗo an zaɓe shi sanata ne a jam’iyar APC 2023 a jam’iyar ne zai nemi kujerar Gwamnan Sokoto a halin da ake ciki shi ne mutum na farko da ya fara bayyana neman takarar kujerar cikin kwanciyar su ta APC.

Sanata ya fitar da ƙudirinsa ta hannun jami’insa da ke kula da harkokin yaɗa labarai Auwal Nasir in da ya ɗora fostar takarar a turakarsa ta facebook.

Fitar da fostar ke nuna cewa Sanatan zai shiga zaɓen fitar da gwani na jam’iyar in da ake hasashen zai kara da Gwamnan Sokoto Ahmed Aliyu wanda shi ma ake da ran zai nemi tsayawa takarar don ya sake zama Gwamna a karo na biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here