Home Siyasa Fayemi ya ƙaryata rahoton ganawar sirri da Kwankwaso

Fayemi ya ƙaryata rahoton ganawar sirri da Kwankwaso

10
0

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, ya ƙaryata rahotannin da ke ikirarin cewa ya yi wata ganawa ta sirri da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa da ke Abuja.

A wata sanarwa da Shugaban sashen hulɗa da Jama’a na ofishinsa, Ahmad Sajoh, ya fitar, Fayemi ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, tare da buƙatar jama’a su yi watsi da shi.

Sanarwar ta ce Fayemi ya haɗu da Kwankwaso sau ɗaya kacal a cikin shekarar da ta gabata, kuma hakan ya faru ne a wajen ƙaddamar da littafi a bainar jama’a, ba a wata ganawar siyasa ta sirri ba.

Fayemi ya jaddada cewa dangantakarsa da Kwankwaso ta ta’allaka ne kan abota da girmamawa juna, ba tare da wata alaƙar siyasa ba, yana mai sake tabbatar da jajircewarsa ga haɗin kan ƙasa da tattaunawa mai ma’ana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here