Mutanen garin Tiɗibale a ƙaramar hukumar Isa a jihar Sakkwato bayan sun ƙauracewa garin kwana huɗu sun amince gwamnatin Sakkwato ta mayar da su gida in har za a samar da tsaro na dindin a yankin.
‘Yan bindigar sukan zo su karɓi kuɗi a hannunsu amma sai suka ga lamarin ya sauya bayan sun haɗa kuɗi kusan miliyan 20 domin a bar su, su yi noman damina da ya gabata, amma maharan suka cigaba da ɗaukarsu da kashe su hakan ya sa mai garin ya ce su dawo garin Isa domin hankalin gwamnati ya karkato kansu a ɗauki mataki na kawo masu ɗaukin gaggawa.
Garin Tiɗibale da Toshe da wasu garuruwa rikon su, sun aminta da su sake komawa garuruwansu kamar yadda gwamnati ta buƙata, an fara jigilar su ne tun jiya Laraba, Alhamis mota ta fi 30 da aka ɗauki mutane zuwa can .
Malam Ibrahim Tiɗibale ya ce ya zo garin Isa ne don tseratar da rayuwarsa “ɓarayi ne suka matsa mana suna fatattakar mu suna aza mana kuɗin fansa da garkuwa da mu shi ne tashin hankalinmu ya sa muka watse a Tiɗibale saboda barazana.”Mun watsu daban daban amma in da muka fi yawa shi ne garin Isa, akwai wasu a Goronyo akwai su Shinkafi da Mai lalle da Sabon Birni, wasu sun tafi da iyalansu a kudancin Nijeriya,” a cewarsa.Kan maganar komawa garin ya ce “gwamnati da jami’an tsaro sun fara mayar da mutane can kuma an ce an kai jami’an tsaro, mun amine mu koma in har za a samar da tsaro a yankin gaba ɗaya.”Samar da mafita sai Allah, muna jira mu gani in ba barazana ba ce daga baya za a jaye jami’an tsaron, mu dai Allah ya ba mu tsaro ya shiga cikin lamarinmu mu zauna a gidajenmu.”Ya ce sun kai kwana huɗu da barin gudajensu amma yana fatan ya koma domin gaba daya sai da Tiɗibale ta watse gaba ɗaya.”Kira na ga gwamnati a taimaka a samar da zaman lafiya ga yankinmu shi ne buƙatar mu,” a cewarsa.
Sarkin Arewan Tiɗibale ya ce sun baro garin su ne saboda ɓarayi sun kore su a kwanan baya sun shiga gidana da Asuba da zimmar za su tafi da ni “suka ce mun zo mu ɗauke ka na ce nikam ban ɗaukuwa sai dai ku kashe ni, abubuwan da ke cikin ɗakina na amfani duka suka kwashe ana haka suka ji kukan mota suka ɗauka sojoji ne anan suka tsere.”Bayan nan muka yanke shawarar a bar garin yanzu haka sun yi garkuwa da mutane 9 namu suna hannun su.”Kan maganar mayar da su gida da gwamnati ke yi ya ce sun aminta da hakan tunda ga jami’an tsaro za su zauna da mu.
Gwamnatin Sakkwato a wani jawabi da daraktan yaɗa labari na gwamna Abubakar Bawa ya fitar ya ce gwamnatin Sakkwato ta samu labarin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna wasu mutane tare da ikirarin cewa mazauna ƙauyen Tiɗibale ne da ‘yan bindiga suka kore su daga gidajensu.
Gwamnatin J na son ta fayyace a sarari cewa mutanen da ke cikin bidiyon hakika mazauna kauyen Tidibale ne da ke cikin Karamar Hukumar Isa, amma ba ‘yan bindiga ne suka kore su ba. An dai kawo su ne na ɗan lokaci zuwa hedkwatar Karamar Hukumar Isa bisa shawarar hukumomin karamar hukuma, sakamakon jita-jitar da ta yadu cewa ‘yan bindiga na shirin kai hari kan yankin.
Da samun wannan bayani, wanda ya janyo fargaba da tashin hankali a zukatan al’umma, wakilin mazabar yankin, Honarabul Dayyabu Sani, ya gaggauta sanar da Shugaban Karamar Hukumar Isa, Alhaji Sherifu Kamarawa. Nan take, Shugaban Karamar Hukumar ya bayar da umarnin a kwashe mutanen kauyen na wucin gadi zuwa hedkwatar karamar hukumar a matsayin matakin kariya.
An mayar da mazauna kauyen Tidibale zuwa gidajensu na gado cikin koshin lafiya, yayin da hukumomin tsaro suka ƙara tsaurara sintiri a yankin domin hana duk wani yunkurin tayar da zaune tsaye daga ɓata-gari.
Domin ƙara tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a kauyen Tidibale da ma kewaye, Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da kafa sansanin tsaro na gaba (Forward Operations Base – FOB) a yankin, domin ƙarfafa tsare-tsaren tsaro da ke gudana a Karamar Hukumar Isa.
Gwamnatin Jiha na jaddada wa al’ummar jihar, musamman waɗanda ke yankunan da ke fuskantar ƙalubalen tsaro, cewa tana da cikakken ƙuduri na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a kowane lokaci.
Gwamnatin za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro na ƙasa, Hukumar Tsaron Al’umma ta Jihar, da kuma kungiyoyin sa-kai, domin kare al’ummomin karkara a faɗin jihar.
Haka kuma, gwamnati na gargaɗin jama’a da su guji siyasantar da batutuwan tsaro, tare da kira ga ‘yan ƙasa da su ba da cikakken haɗin kai ga gwamnati da hukumomin tsaro wajen yaƙi da ‘yan bindiga, ciki har da fallasa masu ba su labari da ke zaune a cikin al’umma.
Bugu da ƙari, an shawarci jama’a da su guji yaɗa jita-jita, musamman waɗanda suka shafi tsaro, sakamakon irin fargaba da ruɗani da suke haifarwa.






