Home Rahoto An kama sarauyi bisa yunƙurin baiwa ɗaurarru tabar wiwi a cikin burodi...

An kama sarauyi bisa yunƙurin baiwa ɗaurarru tabar wiwi a cikin burodi a Kano

2
0

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCoS), reshen jihar Kano ta baiyana cewa jami’an ta da ke aiki a gidan gyaran hali na Gwauron Dutse sun cafke wani matashi bisa yunƙurin bada tabar wiwi ga ɗaurarru a jihar

A sanarwar da Kakakin NCoS, CD Musbahu Lawan K/Nassarawa ya fitar a yau Alhamis a Kano, an kama matashin mai suna Muhammad Kabir dan unguwar Hotoro Tishama da tabar wiwi din kunshe a cikin burodi.

A cewar CSC K/Nassarawa, an kama matashin ne a harabar babbar kotun jiha yayin da ya ke yunkurin baiwa ɗaurarru wiwi bayan an kawo su kotun domin yi musu Shari’a.

Kakakin ya ce tuni dai Kwantarola na NCoS na Kano, Ado Inuwa ya bada umarnin miƙa matashin zuwa hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here