Fargaba da zaman ɗar-ɗar sun sake dawowa a kauyen Tidibale, wani ƙaramin ƙauyen manoma da ke gabashin Karamar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato. Mutanen garin sun fara fargabar abin da zai iya zuwa ya dawo bayan fitaccen jagoran ’yan bindiga, Bello Turji ya fitar da wata barazana mai tsanani ga al’ummar yankin.
A rahoton da Vanguard ta wallafa yau Talata, ta ce mazauna yankin sun ce barazanar, wadda ta zo bayan dogon lokaci da daina jin duriyar Turji, ta jefa jama’a cikin tsoro mai tsanani.
An ce a karshen makon nan, iyalai da dama sun fara barin gidajensu da gonakinsu, suna tafiya zuwa wuraren da suka fi tsaro domin tsira da rayukansu. Wasu mazauna kauyen sun gudu zuwa garin Isa, Gidan Hamisu, yayin da wasu suka tsallaka zuwa Shinkafi a Jihar Zamfara domin neman mafaka. Rahotanni daga yankin na nuni da cewa Bello Turji na ƙoƙarin sake nuna ƙarfinsa da tasirinsa bayan dauke kafar da ya yi a kwanakin baya.
An ce kasurgumin dan bindigar ya turo sakon barazana cewa duk al’ummomin da suka ki masa biyayya ko jituwa da shi za su fuskanci mummunan sakamako.
Mata, yara da tsofaffi na daga cikin waɗanda suka bar matsugunansu, yayin da manoma da ya kamata su fara shirin noman badi suka koma kwana a gidajen ’yan uwa ko tantuna na wucin-gadi, ba tare da tabbacin lokacin da za su koma gida ba.



