Home Ra'ayi Mi ya sa janyen tallafin Man Fetur bai hana Gwamnatin Tinubu ciwo...

Mi ya sa janyen tallafin Man Fetur bai hana Gwamnatin Tinubu ciwo bashi ba?

10
0

Mi ya sa janyen tallafin Man Fetur bai hana Gwamnatin Tinubu ciwo bashi ba?

Har yanzu wasu ƴan Najeriya na mamaki kan dalilan da suka sanya gwamnatin ƙasar ta ci gaba da cin bashi daga waje da kuma cikin gida duk kuwa da janye tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

A yayin sanar da janye tallafin man fetur da ya yi a lokacin shan rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasar, ranar 29 ga watan Mayun 2023, Shugaba Bola Tinubu ya ce za a karkatar da kuɗaɗen don gudanar da wasu muhimman ayyuka.

Shugaba Tinubu ya koka cewa tallafin man fetur da gwamnati ke biya na janye ɗumbin dukiyar da ya kamata a yi amfani da ita wajen samar da muhimman abubuwan more rayuwa a ƙasar.

To sai dai tun bayan hawansa mulki shekara uku da suka gabata, Shugaba Tinubu ya ci manyan basuka aƙalla takwas.

Wani abu da ya riƙa dasa ayar tambayar cewa ina kuɗin tallafin da gwamnatin ta janye da ta ce zai ishe ta gudanar da wasu muhimman ayyukan?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here