Home Siyasa APC:Bance Ina Goyon Bayan Gwamna Abba Kabir ba -Kwankwaso

APC:Bance Ina Goyon Bayan Gwamna Abba Kabir ba -Kwankwaso

5
0

An ja hankalin jama’a kan wani rahoto mai ruɗani da kafar Premium Times ta wallafa, inda ta yi iƙirarin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya amince ko ya goyi bayan cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai koma jam’iyyar APC.

Mun sanar da jama’a ba tare da shakka ba cewa wannan rahoto ƙarya ce, ruɗani ne, kuma ba shi da tushe ko hujja.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayinsa na Shugaban Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na ƙasa, yana nan daram kan manufofi, akida da hangen nesa na jam’iyyar.

Haka kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf an zaɓe shi ne a ƙarƙashin tutar NNPP, kuma har yanzu cikakken mamba ne na jam’iyyar, tare da alhakin kare amanar da al’ummar Kano suka ba shi.

A ko wane lokaci, Sanata Kwankwaso bai taɓa amincewa, goyon baya ko bayyana yardarsa ga duk wani zargin shirin Gwamna Yusuf na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba. Duk wani rahoto da ke nuna haka ƙirƙira ce ta gangan.

Saboda haka, muna kira ga jama’a, magoya baya da kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da wannan jita-jita, su dogara da tushen labarai ingantattu kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here