Home Uncategorized Ƙungiyar Manoma Ta Buƙaci Gwamnati Ta Tallafa wa Manoman Rani da Famfunan...

Ƙungiyar Manoma Ta Buƙaci Gwamnati Ta Tallafa wa Manoman Rani da Famfunan Solar

7
0

Ƙungiyar Manoma Ta Buƙaci Gwamnati Ta Tallafa wa Manoman Rani da Famfunan Solar — Ta Hannun Sabon Shugaba, Mohammed Magaji Gettaɗo

Ƙungiyar Manoman Nijeriya (AFAN) ta buƙaci gwamnatocin Tarayya da na jihohi da su gaggauta tallafa wa manoman ƙasar nan da kayan aikin noma na zamani, musamman famfunan ban ruwa masu amfani da hasken rana (solar), domin bunƙasa noman rani da kuma rage dogaro da man fetur da dizal.

Ƙungiyar ta bayyana cewa manoman Nijeriya sun tafka asarar mai yawa a noman daminar da ta gabata, sakamakon faɗuwar darajar amfanin gona, tsadar takin zamani, da kuma hauhawar farashin magungunan feshi. AFAN ta ce duk da cewa manoma ba su da wata matsala idan sun sayar da amfanin gonarsu a farashi mai sauƙi, to, ya kamata a sauƙaƙa musu hanyar samun kayan noma ta hanyar rangwame da tallafin gwamnati.

Sabon Shugaban ƙungiyar AFAN na ƙasa, Honorabul Mohammed Magaji Gettaɗo, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya fara da yin tsokaci kan irin asarar da manoman ƙasar nan suka fuskanta.

Honorabul Gettaɗo ya ce AFAN ta daɗe tana jan hankalin gwamnati kan wannan matsala tun kafin ta yi kamari, inda ya bayyana cewa burin ƙungiyar shi ne a tabbatar da cewa abinci ya yi sauƙi ga al’umma, yayin da manomi kuma yake samun riba.

Ya ce idan manomi ya samu taki a farashin Naira dubu 10 zuwa 15, sannan ya sayar da masararsa a farashi mai kyau, to ba zai shiga asara ba. A cewarsa, idan aka sayar da buhun masara a tsakanin Naira dubu 15 zuwa 20, manomi zai iya sayen takin zamani buhu biyu daga amfanin da ya girba, wanda hakan zai amfani manomi da kuma al’umma baki ɗaya.

Gettaɗo ya jaddada cewa noman noma ne ke ɗaukar kusan kashi 75 cikin 100 na ayyukan yi a Nijeriya, don haka duk wani tallafi da aka bai wa manoma, kai tsaye al’umma ce ke cin gajiyarsa.

Dangane da hanyoyin aiwatar da hakan, Shugaban AFAN ya buƙaci gwamnati ta koma tsarin da aka saba amfani da shi a baya, na sayen amfanin gona kai tsaye daga manomi a lokacin girbi, ba bayan watanni huɗu ko biyar ba.

Ya ce AFAN ba ta goyon bayan sayen abinci daga hannun manoma bayan ya riga ya fita daga hannunsu, domin a cewarsa, lokacin girbi ne manomi ya fi buƙatar tallafi. Ya ba da shawarar cewa gwamnati ta sayi amfanin gona a lokacin da kason danshinsa bai wuce kashi 13 cikin 100 ba, a ajiye shi a rumbuna, sannan a fitar da shi ga jama’a a lokacin da ake buƙata a kan farashi mai sauƙi.

Honorabul Gettaɗo ya kuma buƙaci a rage wa manoma wahalhalun da suke fuskanta wajen kai amfanin gonarsu kasuwa, ciki har da haraji da kuɗaɗen mamomi. Ya ce idan manomi ya kai amfanin gonarsa kasuwa, bai kamata a karɓi haraji daga gare shi ba, sai dai daga wanda ya saya.

Ya ce irin wannan tsari zai ƙarfafa manoma, tare da rage musu asara, yana mai tunawa da yadda aka taɓa aiwatar da irin wannan tsarin a zamanin gwamnatin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo.

Gettaɗo ya bayyana cewa AFAN ta taɓa samun nasarar samar wa manoma bashi ta Bankin Manoma, inda aka bai wa manoma rancen kuɗi tsakanin Naira dubu 150 zuwa 200, tare da yi musu inshora. Ya ce duk manomin da ya fuskanci ambaliyar ruwa ko fari, an biya masa diyya ta banki.

Dangane da rabon takin zamani, Shugaban AFAN ya yabawa ƙoƙarin gwamnatocin Tarayya da jihohi, amma ya ce babbar matsalar ita ce rashin bayar da taki a kan lokaci. Ya ba da shawarar cewa dukkan jihohi su riƙa ƙaddamar da rabon taki a lokaci guda, misali daga 1 zuwa 15 ga watan Mayu, domin rage tsadar taki da hana ‘yan kwangila sayar da shi zuwa wasu jihohi.

Honorabul Gettaɗo ya ce a wannan wa’adin shugabancinsa, AFAN za ta tabbatar da cewa ba a ƙara karɓar kuɗi daga manoma da sunan fom ko tallafi ba. Ya ce ƙungiyar za ta yi wa dukkan manomanta rajista tare da “mapping” gonakinsu, domin tabbatar da cewa tallafi yana zuwa ne ga manoma na gaskiya, ba ‘yan damfara ba.

A ƙarshe, Shugaban AFAN ya jaddada muhimmancin noman rani, yana mai cewa shi ne ke samar da abinci fiye da yadda ake zato. Ya ce amfani da famfunan ban ruwa masu amfani da fetur ko dizal ya zama mai tsada sosai, don haka AFAN na roƙon gwamnati ta sayi famfunan solar da yawa domin raba wa manoman rani.

Ya ce noman rani na samar da ayyukan yi ga matasa da dama, inda ya kawo misalin yadda matasa a jihar Gombe ke barin mashinansu suna shiga gonaki domin noman rani, ciki har da noman dankali, gurom da sauran amfanin gona.

A cewarsa, abin da manoman ke nema kawai shi ne tallafin gwamnatocin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi, domin bunƙasa noman rani da samar da wadataccen abinci ga ’yan Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here