Daga Ukasha Ibrahim.
Kotu ta rushe zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Adamawa wanda Nuhu Ribadu yashigar da kara inda yake kalubalantar nasarar da Senata Aisha Binani tasamu na lashe gwani a zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam’iyar APC.
Mai shari a justice AbdulAziz Anka wanda shine ya jagorancin shari ar ya karanto tuhume-tuhumen da kuma hukuncin da kotu ta yanke ne kamar haka :
1. Batu kan amfani da kudi yayin zabe :
Kotu ta yi watsi da maganar da ake cewa “yar takarar Gwamna senata Aisha Binani tayi amfani da kudi domin juya zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Adamawa karkashin jam’iyar APC
2. Batu amfani da kudi domin sayan masu kada kuri u daga karamar hukumar Lamurde:
Kotu tayi watsi da hujjojin da bangaren masu kara suka gabatar gareta na cewa “yar takarar gwamnan jihar Adamawa senata Aisha Binani tayi amfani da kudi wurin sayan masu ka’da ‘kuri u na Karamar hukumar lamurde
3 . Batu kan aringizon kuri u a yayin zabe :
Mai shari a AbdulAziz Anka yace wanan matsala ce daga wurin masu tantance masu ‘kada kuri u ba laifin “yar takara senata Aisha Binani bane
A karshe dai kotun tarayya dake Yola fadar jihar Adamawa karkashin jagorancin mai Shari a AbdulAziz Anka ta rushe zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Adamawa wanda jam’iyar APC ta gudanar sanan ta bada umarnin sake yin sabon zabe anan da sati 2 masu zuwa





