Atiku Ya Shilla Turai a Wata Tafiyar Kasuwanci Ba Shan Magani Ba
Awanni bayan sanar da mambobin tawagar kamfen dinsa na takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar zai tafi turai wani taro mai muhimmanci.
Rahoton da muka samo daga jaridar Vanguard ya ce, Atiku zai tafi turai ne domin halartar wani zama na harkallar kasuwancinsa.
Tafiyar dai zai yi ta ne a yau Juma’a 16 ga watan Satumba, kamar yadda sanarwar ta bayyana, rahoton Daily Trust.
“Tafiyar yau cigaba ce ga tafiyar kasuwancin farko a makwanni 3 da suka gabata.
“A karshen tafiyar sa Turai, tsohon mataimakin shugaban kasar zai kuma yi amfani da damar don ziyartar iyalinsa a Dubai.
“Tafiya dai ta kasuwanci da kuma ganawa da iyali kuma ba ta da alaka da batun lafiya kamar yadda wasu ke yadawa.”





