IRISH SALAD
INGREDIENTS
Irish
Egg
METHOD
Dafarko zaki samu dankalin turawar ki ki fere ki wanke kisa a wuta da ɗan gishiri,ya dahu luf se ki sauke,
Ki juye shi a matsami,se ki ɗaura ƙwanki a wuta shima ya dahu,se ki samu dankalin da luddayi ki daddana shi sama sama,se ki yayyanka dafaffen ƙwanki,ko ki daddana, zaki iya ci haka ko da shinkafa ko kus kus.
Wannan hadi ne na zamani da zai taimai mace a wurin iya girki daban-daban a lokaci-lokaci na musamman domin kayatar da iyali.
Ki gwada wannan hadi da sauran wadanda muke samarwa a wannan kafar za ki matukar shan mamaki a tsakanin iyalanki da danginki da suke cin abincinki.
Girki na cikin abin da ke sanya mace ta zama cikakkiya a tsarin mata masu aji da daraja.
MRSBASAKKWACE.





