Daga Ukasha Ibrahim
Majalisar dokokin jihar Adamawa ta amince da kudirin gwajin yin shaye-shaye yayin neman aiki ko kuma neman shiga makarantar gaba da Sikandare a kaf fadin jihar.
Kudirin wanda dan majalisa mai wakiltar Yola ta kudu, Honarabul Kabiru Mijinyawa ya gabatar gaban majalisar wanda zai tilastawa masu neman aiki da masu bukatar shiga manyan makarantu a jihar ta Adamawa yin gwajin shan giya ko shan miyagun kwayoyi kafin daukar su aiki ko kuma shiga manyan makarantu,
Kudirin dai ya samu marawar mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar mai wakiltar Gombi Hon. Japhet Kefas
Bayan aminta da kudirin, kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, Rt. Hon. Iya Abbas ya bada umarnin fara yin shiri domin mikawa gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri wanan kudirin domin sa hannu, kamar yadda shashin Yola 24 English ta ruwaito.






