Home Uncategorized Hukumar Zabe Ta Nijeriya Ta Saka Sabbin Ranakkun Zaben 2023

Hukumar Zabe Ta Nijeriya Ta Saka Sabbin Ranakkun Zaben 2023

9
0

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa waton INEC ta saka sabbin ranakkun zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya da gwamna da ‘yan majalisar jiha a ashekarar 2023.

 

Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana cewa za a yi zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya da suka kunshi sanatoci da ‘yan majalisar tarayya a ranar 25 ga watan Fabarairun 2023.  

Shigaban ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar hakan kuma zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi zai gudana ranar 11 ga watan Maris na 2023 ɗin.

A cewarsa, an zaɓi ranakkun zaben  saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar zaɓe, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar zaɓen aƙalla kwana 260 kafin kaɗa ƙuri’a.

Ya ƙara da cewa hukumar za ta wallafa sauran tanade-tanaden dokar zaɓen “a lokacin da ya dace”.

A jiya ne shugaban kasa ya rattabwa sabuwar dokar zabe hannu abin da ake ganin zai samar da wasu sauye-sauye ga hukumar domin ganin an bi dokar yadda ta tanadar.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here