Home Uncategorized IFI IFI:Babban Hadin Da Duk Macen Da Ba Ta Iya Ba Tana...

IFI IFI:Babban Hadin Da Duk Macen Da Ba Ta Iya Ba Tana Da Saura A Girki

8
0
BASAKKWACE’Z KITCHEN
 
      
 
IFI IFI
 
INGREDIENTS
1.fulawa
2.dakakken nama
3.kwai
4.attaruhu,albasa
5.magi,gishiri
6.yeast
7.garin tafarnuwa
8.curry
9.butter
 
 
METHOD
Za ki kwaba fulawar ki da yeast da dan magi da curry da kuma butter,sai ki bata kamar minti 30 haka,dama kin daka namanki bayan kin dafa shi da albasa da magi da garin tafarnuwa, sai ki jajjaga attaruhu da albasa ki zuba a ciki kisa maggi,gishiri da curry da tafarnuwa ki jujjuya, san nan ki dauko fulawar nan ki dinga yanka kina murzawa,amma kiyi saman me fadi kasan kuma siriri yadda ze nadu sosai sai ki dauko wannan hadin ki dinga diba kina zubawa akan wajan fadin dama kin dafa kwanki kin bareshi kin yi masa yanka (slice) sai ki zuba shi shima sai ki dinga nadewa har ya nadu sai ki danne shi da jelar cokali yadda ze zauna sosai,sai ki dauko kadadden kwanki ki shafa a jiki,sai ki gasa a oven, amma idan ze kwana karki saka masa kwai kuma ki soya naman tukunna.
 
 08167151176
MRSBASAKKWACE

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here