Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta ce za ta tura ma’aikatanta dubu 12 don gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin Abuja a 12 ga watan Fabarairu.
Kwamishinan zaɓen Abuja Alhaji Yahaya Bello ya sanar da hakan a Laraba wurin taron masu ruwa da tsaki da ƙungiyoyin sa kai.
Hukumar ta tabbatar da yin adalci a tsakanin ‘yan takara a lokacin zaɓe.
Ya yi kira ga ƙungiyoyin mata su fito don wayar da kan ‘yan ueansu ga yin zaɓen wanda suka cancanta.






