Home Rahoto Ɗan ƙunar baƙin wake ya ta da bam ga sojoji a Borno

Ɗan ƙunar baƙin wake ya ta da bam ga sojoji a Borno

8
0

Wani dan kunar bakin wake ya kutsa da mota cikin ayarin sojoji a yankin Timbuktu Triangle da ke Jihar Borno, inda ya kashe sojoji biyar tare da jikkata wasu da ba a bayyana adadinsu ba.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar wa Daily Trust cewa wasu manyan jami’an soji biyu — Manjo da wani Laftanar sun jikkata a harin.

Ya ce ƴan ta’addan sun yi amfani da mota maƙare da abubuwan fashewa wajen kutsawa cikin ayarin sojojin.

“Har’in ya yi mummunar barna da lalata kayan aikin soji da ake amfani da su wajen hare-haren kai farmaki da kare kai a yayin aikin kawar da ƴan ta’adda da aka kwashe makonni ana yi,” in ji daya daga cikin sojojin.

Rahotanni sun ce sojojin na dawowa ne daga wani aiki a yankin da ya yi nasarar tarwatsa sansanonin ’yan ta’adda da dama tare da kashe da yawa daga cikinsu, lokacin da harin ya faru a kan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here