2027:Sabuwar Doka Tinubu Da Kwankwaso Na Iya Haduwa Da Cikas

2027:Sabuwar Doka Tinubu Da Kwankwaso Na Iya Haduwa Da Cikas

 

Yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma da kuma Kudu maso Kudu za su iya rasa damar tsayar da dan takarar shugaban kasa. 

Wannan ya biyo bayan sabuwar doka da ke Majalisar Dokoki wacce za ta dakile yunkurin yankunan musamman a 2027. 
Punch ta binciko cewa za a tabbatar da dokar ce don bai wa sauran yankuna damar fitar da 'yan takara kamar yadda sauran suka samu dama. 
Dan Majalisa mai wakiltar Apa/Agatu a jihar Benue, Ojema Ojetu shi ya gabatar da kudurin don gyaran fuska a kundin tsarin mulki. Dokar idan ta tabbata za ta dakile yankunan wurin tsayar da dan takara wanda suke yi tun bayan dawowar dimukradiyya a shekarar 1999. 
Har ila yau, dokar ta na neman bai wa yankunan Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya da kuma Kudu maso Gabas damar tsayar da ‘yan takara. 
“Duk yankin da ya samar da shugaban kasa ba zai sake samun damar ba har sai sauran yankunan sun samar da na su shugaban.” 
Wannan zai bai wa sauran yankunan uku damar samun shugaban kasa wanda ba su taba samu ba tun a shekarar 1999. 
Dadi da kari, gwamnonin jihohi ma dole za su bi tsarin inda ko wane yanki ko mazabar Tarayya za ta samu damar fitar da dan takarar gwamna, 9News Nigeria ta tattaro. 
Har ila yau, a bangaren sanatoci ma dole ko wane yanki a mazabar a ba shi damar tsayar da dan takarar sanata ba tare da tauye hakki ba, cewar Spectacle.