Home Siyasa 2027: Ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi na NDC, Ibrahim Kashim, ya fice...

2027: Ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi na NDC, Ibrahim Kashim, ya fice daga jam’iyyar

119
0

Barrista Ibrahim Muhammad Kashim, ɗan takarar gwamnan Jihar Bauchi a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, ya yi murabus daga jam’iyyar nan take.

Kashim ya sanar da murabus ɗinsa ne cikin wasiƙar da ya rubuta a ranar 16 ga Oktoba, 2026, wadda ya aika wa shugaban NDC na Ƙaramar Hukumar Bauchi, sannan ya miƙa wa jaridar LEADERSHIP a ranar Litinin.

A cikin wasiƙar, tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi ya ce ya ɗauki matakin ne bayan zurfafa tunani, bisa dalilai na kansa.

Kashim ya bayyana cewa yana miƙa murabus ɗinsa daga NDC a hukumance, wanda zai fara aiki daga ranar da aka rubuta wasiƙar.

Ya kuma gode wa shugabanni da mambobin jam’iyyar bisa damar da suka ba shi ta kasancewa cikinta.

Haka kuma, ya buƙaci jam’iyyar ta amince da murabus ɗinsa tare da sabunta bayanan da suka shafe shi a kundinta.

Kashim na cikin ’yan takara 15 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta lissafa a matsayin masu neman kujerar gwamnan Bauchi a zaɓen 2027.

A baya, NDC ta tsayar da Kashim a matsayin ɗan takararta na gwamna, yayin da Tata Alhaji yake mataimakinsa a takarar.

Sai dai, Kashim bai bayyana ko zai koma wata jam’iyyar siyasa bayan ficewarsa daga NDC ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here