2027: Umarnin da Aka ba Ministocin Tinubu daga Arewa kan 'Yan Adawa Kafin Zabe

2027: Umarnin da Aka ba Ministocin Tinubu daga Arewa kan 'Yan Adawa Kafin Zabe

 
Wasu ministocin Arewa a gwamnatin Bola Tinubu sun fara fitowa fili don nuna goyon bayansu ga gwamnatinsa. 
Ministocin sun dauki wannan mataki ne duba da yadda 'yan adawa ke sukar gwamnatin ba kakkautawa. 
Punch ta lura da yadda wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati suka fara mayar da martani kan sukar da ake yi wa gwamnatin Tinubu. 
Yayin da sukar ‘yan adawa ke kara karfi, majiya mai tushe ta ce fadar shugaban kasa ta umurci ministoci da ‘yan siyasa su mayar da martani. 
Wani na kusa da ministocin tsaro a majalisar Tinubu ya ce an ba shugabannin Arewa umarni su kalubalanci adawa da ke karuwa kan Shugaban kasa.
Majiyar ta ce: "Ina da tabbacin cewa kwanan nan, kun ga da yawa daga cikin ministocin Tinubu suna fitowa don mayar da martani ga yan adawa.
"Su 'yan tsiraru ne, kuma fadar Shugaban kasa ba su tsorata da su ba, amma mu ma, kuma ina nufin shugabanninmu na siyasa, ministoci da masu an ba mu umarni mu fita filin kamfe don kalubalantar masu suka daga cikin manyan Arewa." 
Wata majiya mai tushe daga fadar Shugaban kasa ta ce banda umarnin da aka ba masu rike da mukaman siyasa na Arewa, an bukaci su sake tallata Shugaban kasa a yankin. 
"Batun ya fi kawai burin Shugaban kasa na 2027, da dama daga cikin ‘yan siyasa daga Arewa da ke cikin gwamnati sun fahimci abin da rashin goyon bayan Tinubu a 2027 zai haifar." 
"Yayin da wasu jiga-jigan siyasa daga Arewa, ciki har da Sanata Wammako da Nasir El-Rufai, ke kokarin hana Tinubu tsayawa takara a 2027, Kashim Shettima, da wasu ministoci suna kokarin ganin shugabancin kasa ya koma Arewa maso Gabas." 
A nata bangaren, fadar Shugaban kasa ta ce ba ta tilasta wa ministocin Arewa su kare Tinubu ba, domin suna yin aikinsu ne kawai.
Mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin labarai da dabaru, Mista Bayo Onanuga, ya ce: "Wadannan ministoci suna yin aikinsu, babu wanda ya umarce su su mayar da martani. 
"Suna aikinsu ne kawai, Idan ka ga mutane da dama suna fadin abin da suka ga dama, dole wani ya mayar da martani ya fadi gaskiya.