2027: PDP Ta Kada Hantar Tinubu da APC, Ta Faɗi Shirinta Na Dawowa Mulki

2027: PDP Ta Kada Hantar Tinubu da APC, Ta Faɗi Shirinta Na Dawowa Mulki
Jamiyyar PDP a Najeriya ta shirya kwace mulkin Najeriya a zaben 2027 da muke tunkara.
Gwamnonin jam'iyyar ne a Najeriya suka bayyana haka inda suka caccaki tsarin mulkin jam'iyyar APC.
Shugaban gwamnonin PDP a Najeriya, Sanata Bala Mohammed na jihar Bauchi shi ya bayyana haka a Jalingo na jihar Taraba a jiya Juma'a 23 ga watan Agustan 2024 cewar TheCable.
 
Gwamnan ya ce mulkin APC ya zama bala'i a Najeriya wanda hakan ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali.
Sanata Bala ya bayyana himmatuwar jam'iyyarsu wurin tabbatar da inganta tattalin arzikin kasar, Tribune ta tattaro. 
 
Ya ce jam'iyyar PDP ta shirya tsaf domin kawo karshen matsalolin Najeriya baki daya cikin kankanin lokaci. Har ila yau, Sanata Bala ya koka kan yadda APC ta wargaza duka abubuwan cigaba da PDP ta samar a cikin shekaru 16 na mulkinta.