Gwamna Umaru Fintiri na Jihar Adamawa ya bayyana goyon bayansa ga takarar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar wajen neman shugabancin Najeriya a ƙarƙashin PDP.
Fintiri ya bayyana haka ne a wurin taron ƙaddamar da neman fitowa takarar Atiku Abubakar a ƙarƙashin PDP, wanda aka ƙaddamar ranar Laraba a Abuja.
Fintiri wanda shi ma ɗan PDP ne, ya ce Atiku ne ya fi dukkan sauran ‘yan takarar kowace jam’iyya cancantar zama shugaban ƙasa, saboda ƙwarewa da gogewarsa da irin faɗi-tashin siyasa da mulkin ƙasa da ya daɗe ya na goyayya.
Gwamnan ƙarara ya nuna rashin gansuwarsa ga takarar da takwaransa na jihar Sakkwato ke yi da kuma ganin yakamata a zaɓi wanda bai kai shekara 60 a duniya.
