2023: Yaushe Ne Mataimakin Gwamnan Sakkwato Zai Kammala Wasar Kwaikwayon Da Yake Yi?

2023: Yaushe Ne Mataimakin Gwamnan Sakkwato Zai Kammala Wasar Kwaikwayon Da Yake Yi?

 

Mataimakin Gwamnan Sakkwato Honarabul Manir Muhammad Dan'iya ya so jam'iyarsa ta PDP ta bashi damar tsayawa takarar Gwamna a zaben 2023, abin da jagorar yafiyarsu a jiha Gwamna Aminu Waziri Tambuwal bai aminta ba, domin yana ganin akwai wanda yafi Dan'iya cancanta a wannan marar.

Tun bayan yanke hukuncin Tambuwal na tsayar da Malam Sa'idu Umar rawa da tafiyar mataimakin Gwamna da magoya bayansa ta canja a harkokin PDP, hakan ya sa kowane mutum mai bibiyar lamurran jam'iyar ke hasaso abin da zai wakana a karshe, wasu na ganin a karshe dai za su bar PDP, wasu kuwa na ganin za su yi ma jam'iyar zagon kasa, wasu na ganin za su bar komi ya wuce su yi aiki don samun nasarar PDP.

A lokacin da PDP da Tambuwal da Wali suka bar mutane da tunani,  ba wata magana ko tsari na fili da aka fito da shi wanda zai nunawa mutane alkiblar tafiyar da za ta rushe wasu hasashe  ta kuma tabbatar da wani.
Manir Muhammad Dan'iya ya fito da wata wasan kwaikwayo a tafiyar siyasarsa, in da aka ga wata alaka da hulda ta zahiri ta bayyana a tsakaninsa da jagoran jam'iyar APC a jiha Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko abin da yakai ga magoya bayansu, ba su adawar juna duk da kujera daya suke takara ta Sanatan Sakkwato ta Arewa.
Da yawan taron da ya hada su za ka ji mutanensu na ambaton "Sai ALU, sai Wali" kai ka dauka Walin yana takarar wata kujera ce daban da Alu.

Tun bayan da PDP ta sauya Honarabul Abdullahi Maigwandu da Manir Dan'iya a takararsa ta kujerar Sanata a zahiri ba a ga Walin yana taro da wasu mutune domin neman goyon bayansu na samu nasarar zabe ba, mafiyawan fostocin da mabiyansa ke likawa suna dauke da sakon "Allah Ga Wali" kalmar da ake ta fassara manufofinta da dama.
Ni da duk wani mai tunani irin nawa suna tambayar kansu yaushe ne wannan wasar kwaikwayon da mataimakin gwamna ke yi za ta kare, ya dauki matsaya daya irin ta siyasa?

Shi ne ya san shirinsa amma manazarta siyasa na kallon lokaci ya yi da yakamata a jingine wannan wasar kwaikwayon in PDP a yi tsaye a yi aiki, in APC a koma a nemi jama'a, in ko da amincewar Tambuwal ake wannan sakar da wahalar gaske hanyar da suka biyo ta bulle masu a karshe.