2023: Takarar Shugaban Kasa Ya Raba PDP Gida Uku

2023: Takarar Shugaban Kasa Ya Raba PDP Gida Uku

 

Neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ya raba jam'iyar adawa a Nijeriya ta PDP gida uku.

Rabuwar ta faru ne kan kasa matsaya da jam'iyar ta yi kan yankin da zai tsayar da shugaban kasa kafin lokacin zaben fitar da gwani da ake tunkara a wata mai kamawa.

Gida na farko a cikin jam'iyar shi ne bangaren tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar wanda ya cike fom na takararsa ta shugaban kasa ya mayar da shi a hidikwatar jam'iya a jiya Litinin tare da magoya bayansa ciki har da gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri da Gwamnan Edo Godwing Obaseki.

Gida na biyu shi ne wadanda suka hadu domin samar da dan takara guda a cikin silhu ba tare da zaben fitar da gwani ba, tsohon shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki da gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da gwamnan Bauchi Bala Muhammad da Hayattudeen ne ke wannan bangaren.

Gida na uku su ne wadanda suka hadu mutanen  Arewa da Kudu suka aminta a yi karba-karba, takarar shugaban kasa a 2023 ta koma kudancin Nijeriya.
Wannan gidan yana karkashin jagorancin gwamnan Rivers Nyesom Wike wanda ya kunshi gwamnoni masu son a yi karba-karba daga Kudu da wasu mutane daga Arewa da ke goya masu baya.

Wasu mambobi dake cikin gidan na uku sun hada da gwamnan Enugu Ifanyi Ugwuanyi da gwamnan Abia Okezie Ikpezu da Oyo Seyi Makinde da Benue Samuel Otom da Sanata Gabriel Suswam tsohon gwamna.

Gwamna Akwa Ibom Udom Emanuel duk da ya sayi fom na takarar shugaban kasa amma har yanzu bai shiga kowane gida ba a yanzu.

Wike ya jagorancin mutanensa sun yi zaman sirri da tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar daga baya tsohon shugaban kasar ya jagorance su zuwa gidan tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida anan ma an yi ganawar sirri ta kusan minti 20.
Ikpezu a madadin sauran gwamnonin da suka yi ziyarar ya ce sun amince da hadin kan kasa ne hakan ya sanya suka zo neman shawara a wurin jagorori domin samar da mafita a abubuwan da kasar ke fama da shi.

Ya ce sun yabawa Babangida kan yanda yake son hadin kan kasa da burinsa na ganin matasa sun karbi jagoranci domin tseratar da Nijeriya.