2023: Ortom da Dattawan Benue Sun Janye Daga Goyon Bayan Dan Takarar Atiku

2023: Ortom da Dattawan Benue Sun Janye Daga Goyon Bayan Dan Takarar Atiku

 

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom a ranar Talata ya bayyana janyewarsa daga goyon bayan dan takarar shugaban kasan jam'iyyarsu ta PDP, Atiku Abubakar. 

Ortom ya zargi Atiku da rashin martaba shi a matsayinsa na gwamna kuma yana tafiya nesa da manufofin jihar Benue da al'ummar jihar, Channels Tv ta ruwaito. 
Wannan martani na Ortom ya zo ne jim kadan bayan da wata tawaga ta dattawan Benue ta Minda Leaders of Thoughts ta bayyana nesanta kanta da takarar Atiku bisa zargisa da yin magana mai tada kiyayya. 
Alamu na nuna cewa, Ortom ya kullaci Atiku ne tun bayan martanina ga wasu kashe-kashe da suka faru a jihar Benue da ake zargin Fulani makiyaya ne suka yi.