Home Daga Marubutanmu 2023: Kwankwaso ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi nazari kan kundin...

2023: Kwankwaso ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi nazari kan kundin manufofin mulkinsa

1
0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya shawarci duk wadanda suka cancanci kada kuri’a a kasar nan da su samu lokaci su yi nazari kan kundin manufofin mulkinsa na neman tabbatar da shugabanci na gari.

 Kwankwaso ya bayar da shawarar ne a jiya Juma’a a Abuja, jim kadan bayan kammala sallar Juma’a a masallacin Al-Habibiyah Islamic Society’s.

Tsohon gwamnan jihar Kano da ya yi wa’adi biyu ya ce akasarin abin da ya yi niyyar yi idan aka zabe shi a matsayin shugaban Nijeriya a 2023 duk su na cikin kundin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, ya ruwaito cewa Kwankwaso, a cikin kundin mai shafuka 160 na manufofinsa mai taken “Alkawari na zuwa gare ku: Tsarin RMK2023”, ya bayyana alkawura 20 da zai cika idan aka zabe shi.

Ya yi alkawarin samar wa ‘yan Nijeriya jagoranci na kishin kasa da cancantar da za a yi amfani da su bisa ka’idojin rayuwar al’umma.

“Za mu yi adalci ga kowa kuma za mu tabbatar da gaskiya da adalci a kowane mataki na mulki,” in ji Mista Kwankwaso.

A nasa bangaren, babban limamin masallacin Al-Habibiyyah, Fuad Adeyemi, ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi da su yi abin da ya dace domin kasar ta daidaita.

A cewarsa, idan dukkan musulmi suka yanke shawarar yin abin da ya dace da taimakon juna, hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.

“Ya kamata mu koyi taimakon juna, mu koyi taimakon juna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here