2023: Buhari Ya Fadi Jerin ‘Yan Takarar da  Zai Marawa Baya

2023: Buhari Ya Fadi Jerin ‘Yan Takarar da  Zai Marawa Baya

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sai ‘yan takaran da jam’iyyar APC ta tsaida kadai zai taya kamfe a zabe mai zuwa na 2023. 

The Nation ta rahoto Garba Shehu yana cewa babu ruwan Mai girma Muhammadu Buhari da tsofaffin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da suka sauya-sheka.
Kamar yadda Malam Shehu ya fada a jawabin da ya fitar a ranar Laraba, shugaban kasar ba zai taya wadanda suka kai APC kotu wajen kamfe ba. 
“Fadar shugaban kasa tana so ta fayyace kuma ta tabbatarwa asalin ‘yan jam’iyyar APC cewa Muhammadu Buhari yana nan da tarbiyarsa ta sojan APC. 
A duka zabe mai zuwa, zai mara baya ne kurum ga ‘yan takaran da jam’iyya ta tsaida, ba wasu ba.