2023: Ba Mu Aminta Da Magoya Bayanmu Su Yi Yawo Da Makami Ba--Sanata Wamakko

2023: Ba Mu Aminta Da Magoya Bayanmu Su Yi Yawo Da Makami Ba--Sanata Wamakko

 

Jagoran jam'iyar APC a jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamako ya yi kira ga magoyan jam'iyar APC a jihar Sakkwato da su yi siyasa ba da gaba ko cin zarafi ba.

Sanata Wammako ya furta hakan ne a gaban magoya bayansa da suka tarbe sa ranar jumu'a a gidansa dake unguwar Gawon Nama jim kadan bayan dawowarsa daga Abuja.

A takardar bayani da mataimaki na musamman ga Sanata Wamakko kan harkokin yada labarai a kafofin sada zumunta na zamani Bashar Abubakar ya sanyawa hannu ya ce a lokacin yawon kamfe akwai bukatar magoya su bi doka da oda ka da kowa ya cire alamar wata jam'iya da ba tasu ba; a cikin jiha.

Haka ma Sanata ya yi kira ga magoya bayansu ka da su yi yawo da makami a lokacin yawon kamfe yin haka sabawa ka'idoji da manufofin jam'iya ne.
Ya nemi magoya baya su cigaba da addu'ar samun nasarar APC a dukkan matakai.