2023: Atiku, Saraki, Da Wike a Yanzu Su Ne Kan Gaba a Samun Tikitin PDP
Jam'iyar PDP nada 'yan takarar shugban kasa 15 da kowanensu ke son jam'iyar ta tsayar da shi don wakiltarta a zaben 2023 dake tafe, da yawan 'yan takarar ba da gaske suke yi ba.
Mutum 15 da za su nemi kuri'un daligate 3,700 bayan Atiku, Saraki, Wike, akawai Bala Mohammed, Aminu Tambuwal, Mohammed Hayatou-Deen, Anyim Pius Anyim, Peter Obi, da Sam Ohunabunwa.
Sauran su ne Emmanuel Udom, Ayodele Fayose, Dele Momodu, Olivia Tarela, ita kadai ce mace a cikinsu, sai Charles Okwudili, Chikwendu Kalu da Cosmos Ndukwe. Kwamitin tantancewa na Mark ya watsar da mutum biyu.
Komar da aka sanya Gwamna Aminu Waziri a cikinta bai fi ya fito daga Arewa maso Yamma ba in da tsohon shugaban kasa a jamhuriya ta biyu Alhaji Shehu Shagari ya fito, ga margayi Ummaru 'Yar'aduwa, sai yanzu kuma shugabn kasa Muhammadu Buhari nakai da wahalar gaske jam'iyar ta sake dauko wani daga yankin a 2023.
Wata majiyar ta ce Tambuwal ya nemawa kan mafita in da ya saye fom na tkarar sanata in da ya baiwa amininsa ya rike masa waton tsohon kwamishinan filaye da gidaje na jiha Aminu Bala Bodinga, don ya yi takarar ya je majalisa ko zai samu shugaban majalisa.
managarciya