2023: An Shigar Da Kara Ta Neman Kotu Ta Hana Rantsar Da Tinubu

2023: An Shigar Da Kara Ta Neman Kotu Ta Hana Rantsar Da Tinubu

An shigar da wata sabuwar ƙara a kotun ɗaukaka ƙara da ke birnin tarayya Abuja, domin hana rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a matsayin sabon shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayun 2023. 

Ƙarar mai lamba CA/CV/259/2023 wacce ɗan takarar jam'iyyar Hope Democratic Party (HDP), Cif Ambrose Albert Owuru, ya shigar tana neman kotun ta bayar da umurni a hana rantsuwar, rahoton Leadership ya tabbatar.
Jam'iyyar tana neman kotun ta hana shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Antoni Janar na tarayya da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), daga rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a ranar 29 ga watan Mayun 2023. 
Jam'iyyar ta fafata a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019, sannan a yanzu tana son shugaba Buhari da AGF da INEC su dakata da ɗaukar wani mataki dangane da zaɓen 2023 wanda ya samar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, cewar rahoton Daily Post
Owuru, wanda ya ke iƙirarin cewa shine a bisa tanadin kundin mulki wanda ya lashe zaɓwn shugaban ƙasa na shekarar 2019, ya haƙiƙance cewa kada a rantsar da Tinubu ko wani magajin shugaba Buhari, tun da shine kundin tsarin mulki ya yarda ya lashe zaɓen 2019 kuma bai yi wa'adin sa ba kamar yadda doka ta tanada. 
Daga cikin abinda ya ke nema, Owuru ya haƙiƙance cewa shugaba Buhari ya yi masa kwacen mulki tun shekarar 2019 saboda kotun koli ba ta yanke hukunci kan ƙarar da ya shigar ba yana ƙalubalantar bayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaɓen. 
Waɗanda aka lissafo a cikin ƙarar sune shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Antoni Janar na tarayya (AGF) da hukumar INEC. Ƙarar wacce Mr Odion Peter ya shigar tuni har an aikewa shugaba Buhari da Antoni Janar na tarayya ta hannun lauyoyin su Mrs Maimuna Lami Ashiru ta ministirin shari'a, yayin da aka miƙa ta hukumar INEC a hannun shugaban sashin shari'a na hukumar, Mr S. O Ibrahim (SAN).