Ɗan majalisar tarayyar Nijeriya mai waƙiltar ƙananan hukumomin Gada da Goronyo Honarabul Bashir Usman Gorau ya rasa hmahaifinsa yana da shekara 78 a duniya.
Alhaji Usman Gorau ya rasu da safiyar Talata bayan ya yi fama da doguwar jinya.
An yi masa sutura kamar yadda addinin musulunci ya tada a ƙauyensu na Gorau dake cikin ƙaramar hukumar Goronyo a jihar Sakkwato.
Margayin yabar mata biyu da ɗiya 22 cikinsu har da ɗan majalisar tarayyar da jikoki da tattaɓa kunne da dama.
Ɗan majalisa Gorau ya bayyana rasuwar mahaifinsa rashi ne babba da suka yi.
“Bango ne ya faɗi a cikin danginmu mun rasa mahaifi uba mun yi rashi sosai.”
Sallar ta samu halarta shugaban jam’iyar PDP na jiha Bello Muhammad Goronyo da wasu ‘yan siyasa da dama.






