Home Siyasa Ƙane ga Sakataren Gwamnatin Zamfara ya koma APC

Ƙane ga Sakataren Gwamnatin Zamfara ya koma APC

2
0

Alhaji Bello Mohammed Nakwada, kanin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Ya Canza Sheka Daga PDP Zuwa Jam’iyyar APC

A wani gagarumin sauyin siyasa gabanin zaben 2027, Alhaji Bello Mohammed Nakwada, kanin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara kuma daya daga cikin masu daukar nauyin yakin neman zaben Gwamna Dauda Lawal a 2023, ya fice daga jam’iyyar PDP mai mulki zuwa APC.

Nakwada ya ce rashin adalci da danniya ga ‘ya’yan jam’iyya ne suka tilasta masa barin PDP, inda ya janye goyon bayansa ga Gwamna Dauda Lawal da kuma dan uwansa, Abubakar Muhammad Nakwada, Sakataren Gwamnatin Jihar.

Haka zalika, Hon. Hassan Idris Gusau, tsohon dan takarar shugabancin karamar hukumar Gusau a karkashin PDP, shima ya koma APC.

An tarbi su tare da magoya bayansu a Abuja inda Ministan Tsaro na Kasa, Dr. Bello Mohammed Matawalle, ya yi masu maraba da zuwa APC. A jawabin sun sun tabbatar da cikakken biyayyarsu ga APC tare da alkawarin yin aiki tukuru don nasarar jam’iyyar. Matawalle ya yi maraba da su tare da kira ga magoya bayansu su shiga rajistar e-registration na jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here