ƘADDARA TA RIGA FATA
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
“G•W•A“`
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE*
*SADAUKARWA WA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER’S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 1*
Re-posting
*BARCELONA
Duk yadda naso nayi bacci abin ya gagara, tsabar farin ciki tun lokacin sallan Asuba bai yiba na shiga toilet nayi wanka na ɗauro alwala, ina fitowa a parlon na kalli ɗakin yadda aka ƙawata mun shi, ni ka ɗai na naji na sake fashewa da dariya, murya a bayyane na furta.
“Wayyo Daddy nah, ni a rayuwa mai zan maka na nuna maka irin farin cikin da ka sakani a rayuwata”? Na faɗa ina maida hannu na da kyau ina ƙara kankame towel ɗina.
Sallaya na shimfiɗa nayi raka’atul fajir, na cigaba da jan carbi inata istighfari, har naji wayata tana sanar dani lokacin sallan Asubah tayi, don tunda zan kwanta Daddy ya karɓi wayana ya saka mun alerm.
Tashi nayi nayi sallan Asubah sannan na zauna ina askhar, fuskana ɗauke da murmushi, ina gamawa na ɗauko qur’ani na, na fara bitan karatu, har saida gari ya fara haske tukun na miƙe na tafi gaban mirrow.
Wata Red dogon riga na nasaka, wanda yayi bala’in fito da kyau na da ƙuruciyata, wanda banfi 16yrs ba, don banfi 5month da cikawa ba, dai-dai lokacin naji muryan Daddy yana ƙirana dai-dai da buga ƙofan da yakeyi.
Da sauri naje na buɗe ƙofan ina dariya na ɗan sunkuyo dai-dai fuskan Daddy ina faɗin, “Good morning my dad,” zaro ido Daddy yayi cikin mamaki yana kallona, a hankali yasa hannu akan haɓan shi yana cewa, “sweet heart har kin shiryah”? Dariya na fara yi ina kallon Daddy nace, “ae nayi 2hrs da shiryawa Daddy”, sannnan na fito daga ɗakin na saka hannu na riƙe na Daddy mukayi hanyan parlon, inda cikin rawan kaina kaman zan koma cikin shi nace, “Daddy kasan daɗin dana ji kuwa? Daddy kullum zan ta maka addu’a Allah ya baka abinda kake so duniya da lahira”, na faɗa ina duban fuskan Daddy da yake ta murmushi.
Muna zama a kan dinning ya dube ni hannun shi riƙe da nawa yace, “sweet heart ni abinda nake so ɗaya zuwa biyu ne a wurinki, na farko ki maida hankali akan abinda ya kawoki kinji?, na biyu kuma ki riƙe mutuncin kanki saboda Allah kinji HUMMAIRAH nah”.
Jikina duk yayi sanyi na ƙura mishi ido, kaman bazan yi magana ba, can kuma sai nace “insha Allahi Daddy bazaka same ni da aikata wani mummunan abu ba, kodan ma…..” sai kuma na sunkuyar da kaina ƙasa ina zubar da hawaye.
Daddy runtse ido yayi kaman shima zai zubar da hawaye, yana girgiza kanshi, can ya dube ni yace, “komai zakiyi sweet heart kiyi shi saboda Allah bawai don kina gudun maganan mutane ba, shi zai sa ki gyara rayuwar ki ko babu idon kowa, kisaka wa ranki Allah yana kallonki kinji”.
Muna gama shan tea, Daddy ya sakani na fito muka fita har bakin titi, wanda tunda muka fito kallon unguwan da muke nakeyi, wanda yayi matuƙar ɗaukan hankalina, kaman Daddy ya san tunanin da nakeyi ya ƙara damƙe hannu na yace, “BOCABELLA, PASSATGE. sunan street ɗin da kike kenan sweet heart, ya miki kyau”?
Murmushin da yake kan fuskana ne ya ƙara wadatuwa, na damƙe hannun Daddy da ƙarfi kaman zanyi tsalle nace, “Daddy na gode wallahi wurin ya mun kyau, kuma insha Allah na maka alƙawari da first class zan dawo maka, bazan taɓa sakaka kaji kunya ba”, na faɗa ina ƙara saurin tafiya ta yadda naga Daddy ma yanayi.
Muna isowa kan titin saiga taxi ya tsaya, Daddy ne yace mishi *UNIVERSITY OF BARCELONA* da sauri na buɗe na shiga na zauna, munkai kusan 30mnt kafin muka isa school ɗin, jikina har wani rawa yake yi tsabar yadda naga school ɗin ya mun kyau.
Da sauri na kalli Daddy ina ɗan murmushi nace, “Daddy school ɗin yayi kyau” shima murmushin kawai yayi ya tare mana wani bus da naga yana shiga cikin school ɗin da student, wani building mai kyau naga mun tsaya, nidai kawai bin Daddy nake har muka shiga wani office mai girman gaske, wani bature ɗan lukuti mai katon tunbi nagani a zaune cikin wannan makeken office ɗin, fuskan shi ɗauke da murna da farin ciki ya taso ya miƙawa Daddy hannu suka gaisa, sannan ya miƙo mun hannu don mu gaisa, amma cikin murmushin da yaƙi barin fuskana, na haɗa hannu na guri ɗaya na matse su a cinyana ina ɗan jujjuya jikina, na amsa mishi gaisuwan shi batare dana miƙa hannu ba, shima dariyan ya ɗanyi yana buga kafaɗan Daddy cikin turancin shi mai daɗin sauraro ya ke cewa Daddy, “Nice doughter ɗin shin”?.
Wuri Daddy ya zauna inda baturen ya nuna mishi, nima gefen Daddy na zauna kaman zan koma cikin shi, haka sukayi ta hira a ƙarshe naga ya ɗaga waya ya ƙira wata yarinya, tana shigowa nagan ta kaman zata ɓalle don rama, har inda yake ta ƙarisa ta gaishe shi, daga nan ya mata bayanin department ɗinmu ɗaya da ita, kuma nima doughter shine, saboda haka ta tafi dani har class ɗin da muke lectures.
Hannu ta miƙo mun cikin sakin fuska, ban ɓata lokaci ba na miƙa mata muka gaisa inda tana riƙe da hannu na tace, “my name is *VICKY*, ina binta da murmushi nace mata, ” *AISHA HUMMAIRAH*” cikin murmushi ta sake cewa, “nice name”.
Daddy sai binmu da murmushi yakeyi har muka fita, inda kafin mu fita na zo na rungume Daddy nace, “Daddy zaka jirani ne”?
yana ɗan dariya ya ɗaura hannun shi a kafaɗa na yace, “zan koma gida akwai abinda zanyi, kina tashi ki nemi taxi ki bashi wannan card ɗin har gidan zasu kawo ki ko sweet heart”, ya faɗa yana bina da kallo har muka fita.
Muna kan hanya vicky take ta bani labarin yadda last week suka fara lectures, da kuma yadda tayi mamakin tana ganewa, domin ita tun a secondry babu abin da take so irin *ACCOUNTING* Nima murmushi nake binta da shi saboda yadda nake son course ɗin, kuma buri na kenan naga na karanta Accounting, don burina naga na zama chartart acoountant wata rana, har class muka isa vicky sai labarin daɗin course ɗin take bani, amma muna dai-dai da zamu shiga class ɗin take gaya mun wahalar wani course wai shi *FINANCIAL ACCOUNTING* amma ita tanaga tsoron lecturer suke ji shiyasa suke ganin kaman da wahala.
Kallonta nayi cikin mamaki nace, “yana baku matsalah ne lecturer”? ɗan ya mutsa fuskanta tayi tana girgiza kanta tace, “no kawai baya dariya ne, kuma yana ɗaukan attendance, kawai dai baya dariya ko kaɗan”.
Haka muka shiga class ɗin, abin mamaki sai naga bamu fi mu 15 ba, cikin mamaki na dubi vicky nake tambaye ta “ina sauran ƴan class ɗin”? Tana murmushi tace mun mu 15 ne dama, amma kusan class uku ne ko wanne 15, sai lokacin exam zamu haɗu dasu a hall ɗaya.
Muna zama bamu fi 5mnt ba sai ga wani lecturer ya shigo, kana ganin shi kaga ɗan gayu, gashi bayida wani tsayi amma sai wani bouncing yake yi, ƙasa-ƙasa vicky tace mun, “mr solomon, yana ɗaukan mu *COST ACCOUNTING* Ina jijjiga kai batare da na dube ta ba na maida hankalina kanshi, abin sha’awa duk da yau na fara shiga class ɗin amma na fahimci lectures ɗin mutumin yadda baku tsammani, inda yamana wani topic *BUDGET CONTROL* gaskiya na gane lecturers ɗin sosai, haka mukayi lectures huɗu a ranan, a ƙarshe mace ce ta shigo ta mana *TAXATION* india ce amma taji turanci na fitar hankali.
har gate muka zo da vicky, inda na samu taxi har gida ya kawo ni, gaskiya na daɗe ina sha’awar kasar spain, inda yau Allah ya kawo ni ɗaya daga cikin state ɗinta, da farin ciki na shigo gidan, daga ɗaki Daddy ya fito yana ware mun hannu, da gudu naje na faɗa jikinshi.
*Masoya novel ɗina wannan karon kumun uzuri ba zan dinga typing kullum ba, haka pages ɗina ba za suna yawa ba, nagode da ƙaunarku*
*HAKA ZALIKA MRS ZERKS BAKI BAZAI IYA FURTA KALMAR GODIYA ZUWA GAREKI BA, NA BAKI KYAUTAR WANNAN SHAFI BESTY NAH, ALLAH YA BAR ƘAUNA*






