NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.
SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI
FAUZIYYA A.A WANNAN SHAFIN NAKI NE, INA ƘARA MIKI TA’AZIYAN RASHIN MIJINKI ALIYU BABAGANA ZAKI (ABBA). TABBAS INA KOKAWA KAINA INA KOKA MIKI RASHIN GWARZON MIJINKI MAI MIKI ƘAUNA FISABILILLAH, INA MIKI ADDU’AN ALLAH YA BAKI MADADIN SHI, ALLAH YA ALBARKACI RAYUWAR HIDAYA, ALLAH YA SA MIKI DANGANA A ZUCIYARKI, TABBAS FAUXY NA TAUSAYA MIKI, HAR YAU ABIN YAƘI BARIN ZUCIYATA.
SHAFI NA 36
__📖 Daidai lokacin su kawu auwal suka shigo daga ɗakin ƙofar gidan shi da uncle Baba, kowan su cikin firgici yake kallon Abba, ganin haka Abba ya buɗi baki yace.
“duk kanku kuyi haƙuri ku zauna a gida, idan naje na dawo sai kuji me yake faruwa, amma yanzu nima bani da tabbacin me ya faru, amma Auwal da Baba su zamuje tare da su, duk yadda ake ciki zan ƙira na sanar da ku”, ya faɗa yana shirin fita daga parlourn.
Ummi ta riƙo hannun shi tana duban shi da kyau tace, ” ba haka naji ka faɗa a waya ba, daga dukkan alamu wani abu ya faru kake ɓoye mana, ko wani abu ya samu Baba Umar ne kam”? ta ƙara sa faɗi hawaye na zubu mata.
Da sauri Aunty hauwa ta matso kusa da Ummi tana zare ido, hannun ta duka biyu akan ƙirjinta, “Ummi nah me kikaji yace ya faru da miji na? Ina fatan dai ba hatsari sukayi ba ko?” sannan ta juya wurin Abba da sauri da yake shirin barin parlourn, hannun shi ta kamo murya na rawa tace, “zan bika naje wurin miji na,” tana jijjiga kai tana hawaye tace, “nikan babu abinda ya faru da mijina, ka kaini gidan mu nagan shi kawai”, ta ƙarasa faɗa jikinta yana rawa sosai.
Kawu auwal ne yazo yakama hannun ta ya miƙawa Mama ita, sannan ya dubi Ummi yace, “haba ummi uwa, keda zaki kwantar wa hankali kuma kece mai son dagula komai? Kuyi haƙuri yadda Abba yace muje duk abinda ake ciki ni da kaina zan ƙiraku ko shi bai ƙira ba” yana gama faɗi yabi bayan Abba da suka fita tunda ya matsar da Aunty Hauwa a jikin shi, suna shiga motan Abba yaja su sai asibitin da aka musu kwatance, suna parking saiga wata motar ƴan custome tana parking a gefen su, Abba zaro ido yayi don ganin shugaban su Baba Umar ya fito da sauri saura suna binshi a baya, ga police sama da goma a asibitin.
Jiki na rawa Abba ya dube su yace, “Allah yasa bai wahala sosai ba, Umar ne suka samu accident a hanyar su, ya faɗa ganin yadda duk suka fita a nutsuwar su, babu wanda ya iya buɗe baki ya amsa mishi sai binshi kawai sukayi zuwa cikin asibitin.
Suna shiga kai tsaye emergency suka wuce inda suka hango yawan ƴan custome ɗin a wurin, da sauri Abba ya ƙarasa, Dr ne da suke tsaye da police ɗin ya ƙaraso gaban Abba, yana duban shi yakaranto mishi number shi na waya, gyaɗa kai Abba yayi alaman shi ne.
Dr dafa kafaɗan Abba yayi yana ce mishi “am sorry sir, munga number ka a wayan shi da sunan ɗan’uwa, kuma kaine last mutumin da kukayi waya da shi, toh ganin faruwar accident ɗin shine muka neme ka, sannan a aljihun shi muka samu I.D Card ɗin shi da ya nuna mana shi custome ne”, sannan ya maida kallon shi kan ogan ƴan custome ɗin yace “mu ƙarasa ku ganshi,” da sauri kowa yabi bayan shi.
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, shi ne kalmar da yake fita daga bakin kowa da ya ɗaura idanu akan Baba Umar da Aunty suwaiba. Jiki na rawa Abba ya ƙarasa kan gawan Aminin na shi kuma ɗan’uwan shi Baba Umar ya kife kanshi a dai-dai inda jini yake ta kwaranya, ya kife yana kuka yana salati iya ƙarfin shi, da ƙyar aka ɗago shi, jiki na rawa ya dubi Dr yace, “meyasa kace mun accident yayi? Yayah kake so na fuskanci dattijon mahaifin mu da wannan mummunan labarin? Yayah ma zanyi na sanar da matar shi wannan batu yadda tun ɗazu bata da nutsuwa? Waye zai iya gayawa ɗiyar shi ƙwalli ɗaya ta rasa mahaifinta data kasa runtsawa a daren yau”? Riƙe shi Kawu auwal yayi yana faɗin kalman “innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”, sannan ya samu wuri ya zaunar da shi, a hankali ya dubi Baba ƙarami da ya kife a ƙasa ya ɗaura hannu akai kaman mace yana ta rusa ihu, gefe ɗaya kuma shugaban su Baba Umar ne da girman shi shima kukan yake tayi baya kallon kowa.
A hankali police ɗin yace,” Anyi abu bai daɗe ba mutanen mu suka ƙarasa wajen, domin jin ƙaran harbi, abinda ya faru wato mun fi tunanin kidnappers ne suka aikata musu hakan, domin alama ya nuna sunƙi tsayawa ne aka harbi mai tuƙa motan, ita kuma matar motar ce data ƙwace suka dinga kifawa, anan kwananta ya ƙare domin babu harbi a tare da ita, saidai wuyanta ya karye, shi kuma ga harbi akan shi kuma ga karaya a kunkuminshi da sauran wurare masu yawan gaske”, bayani Dr shima ya cigaba da yi musu, wanda daga uncle Baba har Abba babu mai fahimta, Kawu Auwal ne kawai yake fahimtan abinda suke faɗa, tare da shugaban su.
Abba basu aka basu gawan ba sai wurin Asuba, inda Abba ya bawa shugaban su Baba Umar number Baban Narabi akan ya gaya mishi, da ƙyar yayiwa Baban Narabi bayanin rasuwa, wanda shi kuma Baban mai ƙarfin imani yayi ta godiya wa ubangiji, sannan yace su taimaka su taho mishi da gawan zuwa jos, yana son a rufe su anan, haka shugaban ya bashi tabbacin zasu aikata.
Shawara Dr ya basu akan a musu wanka a asibitin saboda ɗaga hankalin mutanen gidan, kuma su Abba sukayi na’am da hakan, ma’aikatan asibitin suka wanke gawawwakin, aka shirya su a cikin likkafani, sannan su Abba suka wuce gida domin sanar musu, tunda sukayi parking Abba ya kifa kanshi akan sitiyarin motan ya fashe da kuka, Kawu auwal ne ya saka hannu ya riƙo uncle Baba da ƙarfi ganin zai fita da gudu yaje ya tayar musu da hankali, zaunar da shi yayi yace, “ka zauna a motan bari na fara shiga”.
Yana shiga ya tarar da dukkan mutanen gidan zaune zuru-zuru a parlourn, gefe ɗaya kuma Aunty hauwa ce kwance akan cinyar Mama sai kuka ta keyi, da sauri ta tashi ta nufi kawu auwal, jiki na rawa ta kamo hannun shi tace, “ka kaini wurin miji na yayah auwal, ina sukaje ne shida Aunty suwaiban”?, duk yadda yaso ya daure kawu auwal ɗin sai ya kasa, kawai samun kanshi yayi da fashewa da kuka ya rungume hauwa gam a jikin shi, Addagana ganin haka ya saka ta sunkuyar da kanta tana ta wasa da ƙasan hijabin jikin ta, ga wani haki da ta ke tayi lokaci ɗaya, Ummi ce ta matso jikin su tana tambayan kawu auwal, “ina sauran suke? Me yasamu Baba umar ɗin ne? Ya samu rauni ne sosai”?.
Buɗe ƙofan yasa hankalin kowa ya koma kan Uncle baba da ya kafe a wurin yana kuka kaman ƴa mace, da gudu Aunty hauwa ta je ta rungume shi tana, “ɗan’uwa na kai ne kafi kowa damuwa dani, nasan zaka gaya mun komai, don Allah ina mijina da ƴar’uwata? Sun koma gida lafiya ko”? Uncle Baba yana ɗaga mata kai yace, “tabbas mijinki da ƴar’uwar ki a yau sun koma gidan su na gaskiya, tabbas sun amsa ƙiran ubangijin mu a lokaci ɗaya, sun tafi sun bar mu da tsananin kewar su a zuciyar mu,” ya saka hannu ya dafa shoulder Aunty hauwa ya cigaba da faɗin, “tabbas ƴar’uwata yau kam zuciyar ki ta ƙuna, yau kinyi rashi mafi girma a rayuwar ki, yau kam mun rasa jarumi, nagarin mutum Baba umar da matar shi, sakamakon harbi da ƴan iskan gari suka mishi a hanyar komawa gida, lallai sun jefa zukata dawa cikin maraici ƴar’uwata, Allah yajiƙan su da rahma”.
Komawa da baya da baya Aunty hauwa ta farayi tana bin uncle baba da kallo bakinta a buɗe, har saida tayi tuntuɓe da ƙafan mutum tukun ta tsaya, a hankali ta juya tana bin kowa da kallo, bata iya cewa komai ba bata cigaba da kukan ba, sai ido da take ta buɗewa kaman zasu fito su faɗi ƙasa, a hankali ta riƙe hannun Ummi tace, “Ummi Baba umar da Aunty suwaiba wai sun rasu? Wai sun mutu dukkansu yau, kinsan me Hero yace mun ɗazu? No baki sani bama, ni kaɗai na sani”, sai ta sake hannun Ummi ta juya wurin Addagana da ta fara share hawaye da ƙasan hijabinta, har ƙasa ta tsuguna ta dafa ƙafan Adda tace, “Adda mijina ya rasu, baban ɗiyata wancar”, ta nuna Aisha da ta kwanta a jikin sister Babanta da take ta kuka kaman ranta zai fita, sannan ta dawo da kallon ta kan Adda ta sake cewa, “mijina ya rasu yau, mijin na ya rasu shida suwaiba yau,” sannan ta sake mikewa ba tare da ta furta komai ba, ta tafi gefen Mama ta kwantar da kanta a kafaɗan mama.
“Mama mijina ya rasu ya barni, idan mun tashi za a binne shi a kabari shi kaɗan shi, ni kuma za a dinga ce mun kiyi haƙuri,” ta juyo da fuskar Mama da ta ke ta kuka kaman ranta zai fita tace, “bazan kula kowa ba, zanyi shiru ina kallon kowa, hala mijina yaji tausayi na ya dawo, zan kwanta nayi bacci yanzu”, ta faɗa bayan ta miƙe ta hau kan tree sitter parlourn ta kwanta.
Kowa da yake parlourn kallon Aunty hauwa ya keyi yana kuka na fitar hankali, don duk sun lura abun ya mata yawa ne, har ta rasa tunanin da zatayi, ita kuma Aunty hauwa rufe idon ta tayi gam, Ummi da sauri ta juya tana kallon kawu auwal da ya durƙusa a wurin yana kuka kaman ba shi ba, “auwal ina Abban su ne”? Ba tare da yace mata komai ba ya nuna mata hanyar waje, a guje Ummi tayi hanyar waje.
Bayan sun idar da sallan asuba Abba ya wuce asibiti shida uncle baba, acan suka haɗu da shugaban ƴan custume da wasu abokan Baba Umar, anan aka yi ta shirye-shiyen tafiya da gawawwakin, ba’a ɓata lokaci ba aka gama komai zuwa 9:00am, dukkan su suka shiga jirgi sai jos.
A chan Narabi kuma duk mutanen misau sun iso tun wajajen 9:00 na safe, an cika a ƙofar gidan Baban Narabi, ga mutanen tilde ma duk sun hallara, cikin gida kuma sai kuka mata sukeyi, inda Baban Narabi ya fito ta kofar parlourn shi ya zubawa ƙanwar mahaifiyar Baba Umar da take aure a cikin Narabin da ƙannen Baba Umar ɗin mata da suka rungumeta suna ta kuka kamar ransu zai fita, murya a hankali ya ƙira sunanta.
“Halima! Soyayyar da zaku nunawa Umar kenan? Irin Godiyar da zaku nunawa Ubangijin mu kenan? Don Allah kuyi haƙuri kuyi mishi addu’a don yanzu shi yafi buƙata a gareku, sannan ki kwantar wa yaran da hankali ga shi sun shigo gari da mamatan, kuma zasu shigo dasu cikin gidan domin muga fuskan Umar ɗan aljannah”, ya ƙara faɗi muryan shi yana rawa, a hankali ɗan shi na biyu ya riƙe shi suka fita zuwa ƙofar gidan, domin jin tsayuwar motoci da yawa.
Har cikin parlour aka shigo da gawan su Baba Umar, inda Baban Narabi yace maza iyayen Suwaiba da ƴan’uwan Baba Umar su fara zuwa su gansu su musu addu’a kafin mata su zo.
Ɗaɗɗaya aka dinga zuwa ana musu addu’a, tunda bawai fuskarsu aka rufe ba, duk wanda ya musu addu’a cikin ƙanne da iyayen Baba Umar sai sun zubar da hawaye, Baban Narabi ya sunkuya kan gawan Baba Umar Ya mishi addu’o’i masu yawan gaske, sannan a ƙarshe ya saka hannu ya share hawayen shi yace, “ya kai wannan ɗa mai yawan biyayya a gare ni, ina maka albishir da ni kam mahaifinka na yafe maka duk abinda kake tunani kamun da ga zuwan ka duniya Umar, halinka na gari ya bika har cikin aljannar fiddausi, Umar na yafe maka duniya da lahira, Umar ka tafi ka barni da tarin yawan kewar ka a zuciyata, amma Allahn da ya bani kai yafini sonka, Allah ya maka rahma kai da iyalinka”, ya saka hannu ya shafa fuskan sanna ya miƙe ya koma kan kujera ya zauna yana jan charbi.
A haka iyayen suwaiba da ƙannenta da yayunta mata suka shigo suka mata addu’a, daga nan aka shigo da Aunty hauwa da ta ke rungume a jikin Ummi, da sauran ƴan’uwan Baba Umar mata da umma halima da su umman misau da su Mama, kuma har zuwa lokacin babu hawaye a fuskar Aunty hauwa, gefe ɗaya kuma ƙanwar shi na rungume da Aisha a hannunta.
Umma Halima ce ta sunkuya akan Baba Umar tana kuka, addu’an ma kasawa tayi, ganin haka Mama ta riƙo hannunta ta matsar da ita, tana ta bata haƙuri, Ummi ta riƙo hannun Aunty hauwa har gaban gawan suka durƙusa kusa da fuskar su, murya na rawa tace, “Hauwa kiyiwa mijinki addu’a, ki yafe mishi shi da ƴar’uwar ki.
Murmushi Aunty hauwa tayi tana kallon Ummi tace, “bai mun komai ba, na yafe musu gaba ɗayan su”, “toh ki musu addu’a Hauwa” cewar Baban narabi daga inda yake zaune.
A hankali Aunty hauwa ta dinga yi musu addu’an samun rahma, sannan a ƙarshe ta miƙa hannu aka bata Aisha, ta dubi fuskar Aunty suwaiba ta dubi fuskar Aisha tace, “wannan maman kice ta tafi ta barki ba tare da ta jira girmanki ba, don naso kada tayi kukan rashin haihuwa irin yadda maman mu bata taɓa yi ba, amma sai ta tafi ta barmu tun yanzu, Aisha mun yafewa Aunty suwaiba duniya da lahira, kuma zamuyita mata addu’a har ƙarshen rayuwar mu ko Aisha”? Sannan ta dubi fuskar suwaiba tace, “dama mutuwa zakuyi tare shine kuka mun wayo kuka tafi tare ku kabarni ni kaɗaiko?” ta shafa kan Aunty suwaiba tana share hawaye taja likkafanin ta rufe mata fuska, ƴan’uwan Suwaiba kuma sai kuka sukeyi ganin yadda hauwa ta yi, sannan Aunty hauwa ta juya saitin Baba Umar tace.
“Baba Umar ɗina, zan tamaka addu’a yadda kace, ban san da gaske mutuwar zakayi ba da na biyoku mun tafi tare, bansan me kake so nayi ba babu kai ka tafi kabarni, bayan Ummi zata kula da Aisha, Abba zai maye gurbinka a wurin Baban Narabi, me yasa kuka tafi babu ni? Sannan ta juya ta dubi Baban Narabi wanda lokacin muryanta ya fara rawa tace, “Baba nifa ina son mijina, amma yanzu kowa zai ta cewa mijina ya rasu nayi haƙuri, toh ta yayah zanyi haƙurin?” ta ɗago Aisha ta nuna mishi tace, “Baba sunanta marainiya, ni kuma maman marainiya, Baba ina zan rufe kaina na yita ƙiran mijina da ƙarfi har sai ya tashi? Ina so Baba Umar yaji tausayina ya tashi muyita zama, ni kuma nayita haihuwa ina bawa Aunty suwaiba har yara goma sha biyu, bazan gajji ba, yadda ta keso hakan zanyi,” sannan ta dubi mutanen da ke parloun da suke ta kuka tace.
“kowa ya fita ya barni da su, zanyi ta xama dasu, idan sun tashi sai mu fito tare, amma ina son so, sukuma sun tafi sun barni, bazan iya ba Ummi, bazan iya zama babu su ba , Baba nah”, ta kara sa tana kuka mai ƙarfin gaske, dukkan su ƴan parlourn kuka suke yi, hattah Baban Narabi kukan yakeyi bai hanata maganganun da ta keyi ba.
Bappah ne ya taso daga inda yake ya saka hannu ya ɗago ta daga kan gawan da ta kife a kai tana kuka, bai iya ce mata komai ba, ya miƙar da ita tsaye, suna haɗa ido ya dinga jijjiga mata kai alaman tayi shiru, bai iya cewa komai ba sai hawaye yakeyi, “Bappah miji nane fa kwance a ƙasa wai ya rasu, Bappah kuna nufin mun rabu kenan da shi har abada? Wallahi Bappah ina son mijina sosai, nifa yarinya ce, kaga gawan mijina, amma ga chan mijin Ummi shi bai rasu ba sai nawa, Bappah kai ma fa ka tsufah kaida Baban Narabi amma duk kuna nan sai mijina da bai tsufah ba”, ta rungume Bappan tana kuka mai ƙarfi.
Liman ne ya bada umurnin a fitar da gawawwakin, ana ɗaga su za’a fita Aunty hauwa ta ƙwala ƙara ta faɗi a wurin a sume, lokaci ɗaya kuma Aisha ta saka kuka mai firgitarwa, tana kallon Abba tana “Dada, dada”.
KULLU NAFSIN ZA’I KATUL MAUTI, TABBAS DUK MAI RAI SAI YA ƊANƊANA ZAFIN MUTUWA, HAKA SHI ZAFIN MUTUWA BAYA FITA A ZUCIYAR MU DUK TSAWON SHEKARU, WAYYO MUTUWAR MIJI AKWAI CIWO SOSAI
FAUZIYA A.A, WANNAN SHAFI NAKI NE, DOMIN TUNAWA DANAKEYI NA ZAFIN DA KIKAJI NA RASUWAR MIJINKI ALIYU BABAGANA ZAKI(ABBA)
TUNDA NA FARA PAGE ƊIN NAN KE KIKE FAƊO MUN ARAINA, INA JIN RAƊAƊI A XUCIYATA KAMAR YAU MUKA SAMU LABARIN RASUWAR ABBA, ALLAH YA JIƘANSHI YA MISHI RAHMA, ALLAH YA ƘARA MANA HAƘURI AKAN RASHIN MAZAJEN MU, IYAYEN ƳAƳAN MU, ABIN AlFAHARIN MU 😭😭😭😭😭
