MOMMYN MUSAB SPECIAL GROUP ONLINE TRAINING
&
GYARAN JIKI
Waɗannan ƙwayoyin cuta idan suka samu damar shiga jikin mace
Suna yin kokari suga sunkai ga
1)Uterus
2)ovaries
3)cervix
4)endometrium
5)fallopian tube
Wanda waɗannnan su ne abubuwan da cikin al’aurar mace ya ƙunsa wanda sanadiyar kamuwar cuta da da ya danganci waɗannan tau yana iya kawo matsala kamar haka:
1)rashin haihuwa
2)yawan zubar jini
3)yawan zubewan ciki
4)rashin ganin jinin al’ada
5) ciwon mara
6)Zafi lokacin saduwa
7)daukewar sha’awa
8)zafi lokacin fitsari da sauransu
Ni maman Mus’ab ina bawa mata shawaran duk ta samu ɗaya daga cikin waɗannan matsalar tau kafin ta fara amfani da wani magani yana da kyau ta je asibiti domin a yi mata gwajin abun da yake damunta kafin tafara shan magani.
Sannan kuma mace ko da ba ta da miji za ta iya kamuwa da ɗayan cutar sai dai an fi samun cututtukan a cikin ma’aurata sai kaɗan ne daga ciki marasa aure ke kamuwa .
Allah ya ba mu lafiya.
Aishatu Musa Sani(Mommyn Mus’ab)
07041105956
Share✅
Edit❌
Comment✅






