Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 31

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 31

28
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 31📑

__📖 Tunda muka zauna nake kwance gefen jikin Daddy nah, amma gaba ɗaya hankali da idon Daddy yana kan Dr Hussain, sai kallon shi yakeyi yana tunanin ina ya taɓa ganin mai irin kamannin shi, haka dai ya haƙura da kallon aka shiga gaisawa.

Abbu sunyi tarya wa Daddy na girmamawa, dole Abbu ya saka Faisal ya zo ya gaida Daddy, Abbu yana kallon Daddy yace, “Alhaji Mohd ko zakaje ka ɗan huta ne kafin zuwa dare muyi abinda ya tara mu? don maganan gaskiya ka ɗauko gajjiya yakamata ka ɗan huta”.

“No babu komai Alhaji, idan babu matsalah ya kamata mu tattauna abinda ya kamata”, Daddy ya faɗa hannunshi ɗaya ya na dafe dakai na, amma yawanci idon shi yana kan Dr, wanda gaba ɗaya Dr yakasa sakewa.

Cikin mutsuwa Abbu ya lallaɓa Daddy, babu yadda ya iya haka ya haƙura akabar zaman sai anyi sallan ishaa.

Ana idar da sallan ishaa Daddy da Dr Hussain suka iso gidan, da yake Dr yaja Daddy sun tafi hotel ɗin da ya sauƙa, anan sukayi dinner sannan aka taho cikin main parlon gidan aka zazzauna.

Dubawa Abbu yayi yaga babu Faisal, da hanzari ya ɗauki wayan shi ya ƙira shi, babu ɓata lokacin ya shigo duk jikin shi a sanyaye, gefen ƙafan Abbu yaje ya zauna.

Addu’a Abbu yayi ya buɗe taron da addu’a, sannan ya karanto wa Daddy duk abinda ya faru daga farkon neman mu da Dr har zuwa case ɗinmu da Faisal, da kuma niyyan da Dr yayi na bada labarin shi sai dai yagawa Daddy, daga nan ya fara neman gafaran Daddy na abinda Faisal yaso aikatawa.

Murmushi Daddy yayi ya dubi Abbu yace, “haba Abbu yanzu don wannan tsautsayin da ya faru ne zai saka kayi fushi da Faisal? Ni ae banga laifin Faisal ba sai naku iyayen shi, abinda yasa kuma ɗaya ne, a wannan rayuwa da muke ciki dole ne fah ka hana yaranka maza zuwa sashin yaranka mata, haka zalika suma ƴaƴan mu mata su daina zuwa gefen yayun su mazaa, koda kowa kai musu saƙo ne, domin masifun da yanzu suka mana yawa a duniyar mu, hadda sakacin mu iyaye, wallahi Alhaji zaka sha mamaki idan kaga yadda fyaɗe yayi yawa a wannan lokacin, kuma abin munin sai kaga mahaifi ne yayiwa ɗiyar shi, ko kuma yayah yayi da ƙanwar shi, ko ƙaninka yayi da ɗiyarka ko ƙanin matar ka, munyi sake da barin yaranmu suna chuɗanya kaman jinsun su ɗaya, haka kuma irin suturun da ƴaƴanmu mata suke sakawa a cikin gida, duk yana contributing lalacewan yaran namu, saboda haka mu iyaye mu gyara kafin mu koma kan ƴaƴanmu”.

Daddy ya dawo da kallon shi kan Faisal da yake ta share hawaye yace, “Faisal Amaal da Humairah dukkan su ƙannen kane, tunda Allah ya kiyaye babu abinda ya faru, toh Alhamdulillah, sai dai nace maka don Allah ka ƙara saka tsoron Allah a ranka, kaga nan gaban iyayen kane kayi niyyan aikata haka, toh ina kuma babu idon iyayenka?” Daddy ya daɗe yana mishi nasiha sannan ya nemi kowa ma ya yafewa juna kuma muyi ƙoƙarin kula da zumuncin mu, sannan nima da Amaal ya mana namu faɗan akan mu dinga kula da shigan da zamu dingayi, daga nan ya dawo da duban shi kan Dr Hussain yana murmushi yace.

“Dr Allah bai sa mun taɓa haɗuwa da kai face to face ba sai yau, duk zumuncin mu through phone muke yi, ashe kuma suruki zaka zama mun ban sani ba”, ya ƙarasa faɗi yana murmushi mai kaman dariya, wanda ya nuna tsananin farin cikin Daddy a fuskar shi, kowa da yake cikin parlon saida ya ɗan dara, nidai ban iya darawa ba sai ma ɓoye fuskana da nayi a jikin Daddy, shi kuma Dr ya sake sauƙe idon sho ƙasa.

“Toh Dr Hussain muna saurarenka” cewar Abbu da yake bin Dr da murmushi.

Ƙara tanƙwashe ƙafan shi yayi a ƙasa yana murmushi, kan shi ya ɗago ya kura mun ido yana duba na.

“Alhaji Gambo Aliyu, shi ne mahaifin mu, wanda ya kasance haifeffen garin misau ɗaya daga cikin ƙaramar hukumar Bauchi, misau shi ne asalin garin su mahaifina, sun kasance su uku ne a cikin mahaifansu, yana da yayu guda biyu dukkansu mata, twins ne wato hassana da hussaina, mahaifinmu shi ne Gambon su, wanda sun bashi yakai shekara biyar, bayan an haife sune da shekara biyu suka yi ciwon ƙyanda, inda anan Hassanan Allah yayi mata rasuwa, bayan an haifi mahaifinmu ne suka kasance su biyu kenan a hannun iyayen su, mahaifinsu ɗan kasuwa ne a wancan lokacin, yana kasuwancin shi har zuwa garin jos.

Mahaifina yayi karatu har zuwa matakin digiri, wanda yayi a garin jos inda mahaifinshi yake zuwa kasuwanci, a hannun aminin shi wanda suke kasuwanci da shi ɗan garin Narabi dake jos ya barshi yayi karatu, inda mahaifin mu suka shaƙu da ɗan Baban Narabi mai suna Umar, wanda dukkansu sun kasance masu ilimi sosai.

Goggo Hussaina tayi aurenta a garin misau, amma har zuwa girmanta Allah bai bata haihuwa ba, sai daga baya mijinta ya ƙara aure, inda abokiyar zamantan ta haifi yara kusan huɗu, kuma dukkan su zaka ɗauka Goggo Hussaina ce ta haife su, don tsabar kulawan da ta keyi da su, abin babu wuya Abban mu suna final year a digiri ɗin su Allah yayi rasuwa wa mahaifin su, inda suka shiga cikin tsananin tashin hankali, amma da yake basu da yawa sai Baban Narabi ya ɗauki ɗawainiyar karatun Abba har suka gama.

Abba na lagos aka tura shi service, shi kuma Baba Umar kaduna, haka suka tafi suna kewan junan su.

Bayan 1yr suka gama suka dawo jos, babu ɓata lokaci Baban Narabi ya tsaya kai da ƙafa har saida ya nema musu aiki, inda Abba ya samu aiki da Central Bank, shi kuma Baba Umar ya samu aiki da Custom.

Zuwa wani lokaci komai ya fara musu daidai, sun fara fin ƙarfin komai, sai Abba ya fara neman auren wata yarinya a garin misau, ana shirin auren su Allah yayi mata rasuwa, gaba ɗaya Abba ya shiga cikin wani irin tashin hankali, har sai da yafara kasa aikin shi, ganin haka mahaifiyar shi Umman Misau ta nemi shawaran Goggo Hussaina akan ko zasu bashi auren babbar ƴarsu da yanzu ta gama secondry school a wannan shekaran mai suna FATIMA babu ɓata lokaci Goggo Hussaina ta amince kuma ta bar maganan zata je tayi shawara da iyayen yarinyar, basu wani ja ba dukkansu suka amince inda mijin Goggo Hussaina Alhaji Abubakar dama ya kasance mai matuƙar haƙuri magana ma nan baza kaji shi yana yi ba, malamin gidan gona ne, idan baya wurin aiki toh kullum yana ƙofan masallacin unguwar su da yake manne da gidan shi yana zaune, jama’a da dama suna mutunta shi da halinshi na dattaku, itama mahaifiyar Fatima wato Aishatu itama ba mai magana bace, ta kasance bafulatanan garin gabɗori, duk wanda yasan garin misau ya san gabɗori garin wasu farare kyawawan fulani ne a wurin, gashi ta kasance mai haƙuri da kawaici, ana ƙiranta da suna Addagana, tun ranan da malam Abubakar ya aureta babu wanda zai ce ya taɓa jin tsakaninta da mijinta ko abokiyar zamanta Goggo Hussaina, kuma ta ɗauki iyayen Goggo Hussaina kaman nata iyayen, domin ita ta kasance marainiya ce, babu uwa babu uba, kuma ƴan uwanta sun mata riƙon wahala, toh da ta samu Goggo Hussaina irin mutanen nan ne masu amana da maida ɗan wani nasu, sai ta rungumeta suka zama kaman ƴan’uwa ba kishiyoyi ba, suma iyayen Goggo Hussaina sai suka riƙeta kamar ƴa.

Lokacin da ta haifi Fatima bata cika shekara ba ta samu cikin ɗanta na biyu, dole Goggo Hussaina ta karɓi riƙon Fati ya dawo hannunta, bayan Addagana ta haihu, an samu Muhd Auwal, ko shekara baiyi ba sai ga wani cikin a jikin Addagana, haka Goggo Hussaina ta sake karɓan shi ta haɗa da fatima ta riƙe su, yana da shekara ɗaya da ƴan watanni Addagana ta haifi ɗanta namiji inda Malam Abubakar yayi kara ya saka sunan mahaifin su goggo hussaina wato malam musa, amma suna ƙiran shi da Baba, Addagana wanannan karon bata sake haihuba, don tayi ɓari kusan sau biyu kuma ta haihu kusan sau uku suna komawa, ba ita ta sake haihuwa ba har saida Fatima ta kai shekara goma sha uku, Auwal yana da shekara goma sha biyu, Baba kuma yana da shekara goma da rabi, sai lokacin ta haifi HAUWA

Fatima da hauwa sun kasance suna tsananin kama da mahaifiyar su, domin kana ganin farinsu da gashin su babu abinda suka bari na Addagana, Auwal kuma da Baba duk mahaifinsu suka ɗauka, duk da suma farare ne amma basu yi kyaun su Fatima ba.

Fatima da ƙannenta sun kasance yara masu tarbiya da nutsuwa, domin Goggo Husaina babu abinda ta bari daga tarbiyan su, ta riƙe su kaman ita ta haife su, babu wani mugunta a tarbiyanta, sai kuma yaran suke sonta kaman itace mahaifiyar su, Baba ne kawai wani lokacin sai ya koma ɗakin Addagana, idan sun ɓata kuma ya tattaro ya dawo ɗakin goggo hussaina, kowa zaka ga yana mishi dariya, akan yarasa wurin zama guda ɗaya.

Lokacin da aka gayawa Abban mu maganan auren shi da Fatima bai wani ja ba ya amince, amma ita Fatima sai da tayi ƙorafin ita fa kawun tane kawu Gambo, amma da taga ran Yayah zai ɓaci sai ta amince, da yake haka suke ƙiran Goggo
Hussaina, don duk sunbi bakin Addagana ne.

Ba’a ɗauki lokaci ba akayi auren Abba da Ummi nah, aka kaita garin bauchi inda Abba na yake aiki, sun zauna a wani unguwa wai shi dutsin tanshi, gida ne ɗan madaidaici mai ɗakuna biyu, sai kitchen da wani ɗan store, babu laifi gidan ya dace da sabbin ma’aurata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here