Za Mu Tabbatar Da Hana Ɗauki Ɗora A Cikin Jam’iyarmu Ta APC-----Honarabul Abdullahi Salame

"Don haka duk matakin da aka dauka a zaman ba mu yarda da shi ba, har sai an bi dokokin jam'iya, za mu sabawa duk wanda ya saba dokar jam'iya." a cewar Salame. Honarabul ya yi wadan nan kalamai ne a taron manema labarai da ya kira  a gidansa dake unguwar Bado domin shirye-shiryen zaben shugabanni, amadadin kungiyarsu dake fafutikar samar shugabanci nagari a Sakkwato a 2023 ya ce dole ne a baiwa kowa damar ya yi zaɓe ko a zaɓe sa za mu tabbatar da hana ɗauki ɗora a jam'iyarmu.

Za Mu Tabbatar Da Hana Ɗauki Ɗora A Cikin Jam’iyarmu Ta APC-----Honarabul Abdullahi Salame
Hon. Salame
 

Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela a majalisar tarayya Honarabul Abdullahi Balarabe Salame ya nuna rashin gamsuwarsa ga kalaman shugaban riko na  jam'iyar APC a Sakkwato Alhaji Isah Sadik achida kan cewa sun yi taron masu ruwa da tsaki kan zaben shugabannin dake tafe.
Ya ce wannan taro ne na wani bangare, wasu ne suka yi taronsu na wadan da suke so su kira.
"Ba a gayyace mu ba ni da Kakakin majalisar dokoki wanda shi ne jagoran APC a jiha da sauran mutane da dama da suke jagorori ne a jam'iyar.

"Don haka duk matakin da aka dauka a zaman ba mu yarda da shi ba, har sai an bi dokokin jam'iya, za mu sabawa duk wanda ya saba dokar jam'iya." a cewar Salame.
Honarabul ya yi wadan nan kalamai ne a taron manema labarai da ya kira  a gidansa dake unguwar Bado domin shirye-shiryen zaben shugabanni, amadadin kungiyarsu dake fafutikar samar shugabanci nagari a Sakkwato a 2023 ya ce dole ne a baiwa kowa damar ya yi zaɓe ko a zaɓe sa za mu tabbatar da hana ɗauki ɗora a jam'iyarmu.
Abdullahi Salame ya ce da yawan mutanen da suka nuna shawar tsayawa takara don mutane su duba su zabi nagari kar su kula da cewar wane ne wane ke so su zabi wanda ya cancanta ko jagoransu baya sonsa domin hakan ne kawai zai tseratar da Sakkwato halin da take ciki.

Ya ce za su yi tsaye su tabbatar a jam'iyarsu ta APC wadan da ake so ne aka zaba, domin kawar da siyasar ubangida wadda ke kawo rashin cigaba a jihar Sakkwato.