Yanda Za Ki Haɗa  ZOƁO Mai Ɗankaren Daɗi

             Yanda Za Ki Haɗa  ZOƁO Mai Ɗankaren Daɗi

BASAKKWACE'Z KITCHEN


            ZOBO 


INGREDIENTS
zoborodo 
kaninfari
danyen citta
na'a na'a 
iccen girfa 
bawon Lemun zaki
bawon abarba 
sugar 
ruwa 


METHOD
A zuba zoborodo a wuta a sanya kayan da aka lissafo Daidai ba cikawa ba a zuba ruwa Daidai (ni idan zanyi kadan nakesa ruwan idan nazo tacewa sai na kara ruwa) a barshi ya tafasa sai a tace a zuba sugar idan Ana bukatan flavour za'a iya sawa.

Zoɓo ko soɓo abin sha ne na marmari da yake da matuƙar tasiri a lafiya da nishaɗin mutum.

Mun kawo maku abin sha na zoɓo domin mace ta samar da shi ga iyalanta wanda hakan zai nishaɗantar da su musamman a lokacin da za su ci abinci.

Duk macen da ta iya haɗa zoɓo a gidanta ba ta da takaici a gidanta a fanin abin sha, don wannan haɗin na musamman ne da mutane na musamman ke buƙata ga mace ta musamman a lokaci na musamman.

A sanda kika haɗa zoɓonki kin kyautata lafiyarku gaba ɗaya wurin shan abi tatacce mai inganci a rayuwa.

08167151176
MRSBASAKKWACE.

Sanarwa ta musamman:
DAN ALLAH NUMBER TA DON IN KINA DA TAMBAYA NAKE RUBUTA TA A JIKIN POST,BADON KU YI TA MIN FLASHING BA KUNA CE MIN WAYE,NI BA HAJIYA BA CE KUDE NA MIN FLASHING INNA KIRA IN JI BA MAGANA ME MAHIMMANCI BACE.

INA GODIYA MASOYA DA KULLUM KUKE ƘARA YAWA,WASU SUMIN KIRA WASU MESSAGE WASU SAƘO TA WTSPP,ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI ALLAH YA BAR ZUMUNTA,INA JIN DAƊIN KULAWAR KU GARENI HABIBATIES